Saƙon Tinubu na sabuwar shekara soki-burutsu ne - PDP

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Babbar jam'iyyar hamayya a Najeriya, PDP ta ce jawabin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi wa al'ummar kasar na sabuwar shekara, kalaman baka ne kawai.

A jawabin da Tinubun ya yi ranar Laraba 1 ga watan Janairun, 2025, ya bayyana tsare-tsaren da ya ce gwamnatinsa za ta bullo da su domin rage tsadar farashin abinci da samar da tsaro da kuma wasu nasarori da ya ce gwamnatinsa ta samu.

A dangane da kalaman shugaban ne jam'iyyar PDP ta bakin tsohon sakatarenta na kasa Sanata Umaru Tsauri, ta mayar da martani da cewa kalaman soki-burutsu ne kawai.

A tattaunawarsa da BBC, Tsauri ya ce, abubuwan da shugaban ya karanta abin da su suka dauka an rubuta masa Turanci ne kawai ya karanta, amma ba wai abubuwa ne da suke a zahirin gaskiya ba.

Ya ce duk abubuwan da Tinubun ya fada na cewa gwamnatinsa ta samu nasara, kamata ya yi a ce an gan su a fili muraran, kamar yadda akan ce, ''an ce da kare ana biki a gidanku ya ce to mu gani a kasa.''

Tsauri ya ce duk abubuwan da ya fada ba a takarda ya kamata a gan su ba, yana mai nuni da cewa idan har gaskiya ne gwamnatin ta samu wannan nasara da Tinubun ya fada to jama'a su gani amma lamartin sabanin haka yake.

''Ba abin mamaki ba ne in Shugaban Kasa ya yi wadannan maganganu domin kawai ya sanar da 'yan Najeriya ba don ya dadada masu ba, don duk abin da ya fadi kowa ya sani ba za a ce karya ba ne amma ba gaskiya ba ne - misali in an ce mana farashin mai ya ragu yaushe ya ragu?'' In ji shi.

Ya ce gwamnati na cewa farashin dala ya ragu naira ta kara samun daraja, to amma ya yi nuni da cewa, '' mun wayi gari dala ta koma naira 1600 daga naira 1700, cewa ake an samu nasara, to wace nasara aka samu bayan lokacin da Buhari ya hau mulki muna sayen dala naira tamanin?''

''To wane irin cigaba ne wannan? Mu a wurinmu Turanci ne aka rubuta kuma ya karantu,'' in ji shi.

Dangane da maganar cewa gwamnatin Tinubun ta yi nasara a fannin samar da man fetur, ta hanyar gyara wasu matun mai na kasar, Sanata Umaru, ya ce, '' sati uku da ya wuce aka ce an gyara matatar man Port harcourt kuma kwana biyu aka ce ta sake collapsing, wace magana ce muke yi?''

Ya kara da cewa : ''An gyara matata me muka gani sabo? Saboda haka mu a wurinmu ba magana ba ce ta an gyara mata, amma dan'arewa wanda yake mu daga nan wajenmu ya zai san abin ya yi amfani? Ba gaskiya ba ne. Amma kamar yadda na fadi ba a cewa Shugaban Kasa na karya sai dai mu ce abin da ya fadi ba gaskiya ba ne''

A kan alkawarin da Shugaba Tinubun ya yi na cewa a sabuwar shekarar ta 2025 da aka shiga gwamnatinsa za ta yi kokarin ganin ta rage farashin kayan abinci da sauran abubuwa daga kashi 34.6 zuwa kashi 15 cikin dari, tsohon sakataren na PDP ya ce wannan ma alkawari ne da ba yau aka saba ji ba.

Ya ce tun lokacin Buhari ake wa mutane alkawarin za a saukaka musu rayuwa amma a kullum abin sai karuwa yake.

''Madamar ba a maido da tallafin mai ba duk abin da aka gaya maka labari ake. Idan kudin mai suka karu, wannan abin ya kara kudi. Wanda ke noma masara a gonarshi zai ce ma mai ya kara kudi dala ta kara kudi saboda haka shi ma ya kara kudi,'' a cewarsa.

Dangane da kudurin haraji da gwamnatin Tinubun ta mika wa majalisar dokokin kasar domin samun amincewarta ya zama doka, Sanata Tsauri ya mayar da martani kan bukatar da shugaban ya yi ta neman 'yan kasar su kawar da ra'ayi na bangaranci da kuma siyasa su mara wa kudurin baya.

Ya ce Shugaban ai ba ya bukatar wani goyon baya da hadin kan jama'a domin abu ne da ya kamata a bi doka amma ake neman a yi karfa-karfa a kai.

''In har da gaske ne a yi shi kowa a kira shi ya bayyana abin daya sani game da wannan da abin da ya fahimta illar da ke akwai ka gani, amma an zo da niyyar dama sai ya wuce.'' In ji Alhaji Umaru.

Kudurin dokar harajin dai ya gamu da suka musamman daga yankinarewacin kasar, wanda kuma daman tun da farko majalisar tattalin arzikin kasar wadda mataimakin shugaban kasar ke jagoranta ta bayar da shawarar dakatar da kudurin saboda wasu illoli da take ganin kudurin ka iya yi wa kasa.

Haka kuma ko a baya-bayan nan kungiyar kwadago ta Najeriya ta NLC, ta bukaci shugaba Tinubu ya janye kudurin dokar harajin domin bayar da dama kan sake yin nazari a kai.

Kungiyar ta bayyana hakan ne a cikin sakonta na sabuwar shekara, wanda shugabanta Joe Ajaero ya fitar a ranar Laraba.