Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Arsenal za ta buga wasa tara a cikin Janairun 2025
Ƙungiyar Arsenal ta za ta buga wasa tara a cikin watan Janairu daga cikin gasar Premier League da League Cup da FA Cup da kuma Champions League.
Arsenal wadda take ta ukun teburin Premier League bayan wasa 18 ta ci karawa 10 da canjaras shida aka doke ta fafatawa biyu mai maki 36.
Gunners tana ta uku a teburin Champions League da maki 13, bayan wasa shida da cin karawa huɗu da canjaras ɗaya da rashin nasara wasa ɗaya.
Ranar 1 ga watan Janairu Arsenal za ta fara da zuwa gidan Brentford a karawar Premier League mako na 19 a wasan hamayya na ƙungiyoyin Landan.
Kwana uku tsakani Arsenal za ta sake yin wani wasan Premier League a waje da Brighton daga nan ta karɓi bakuncin Newcastle a League Cup ranar 7 ga watan.
Arsenal za ta kara da Manchester United a FA Cup a Emirates ranar 12 ga watan Janairu, kwana uku tsakani ta kece raini da Tottenham a Premier a Emirates.
Gunners za ta yi wasa na biyar a gida a jere, za ta karɓi bakuncin Aston Villa ranar 18 ga watan Janairu.
Daga nan Arsenal ta kare wasan karshe a Emirates a Janairu da karɓar bakuncin Dinamo Zagareb ranar 22 ga watan a gasar kofin zakarun Turai.
Bayn nan Arsenal za ta yi wasa biyu a waje daga nan ta kammala wasannin cikin watan Janairun 2025.
Gunners za ta je gidan Wolves a Premier League ranar 25 ga watan Janairu, kwana uku tsakani Girona ta karɓi bakuncin Arsenal a Champions League.
Wasa tara da Arsenal za ta buga a cikin watan Janairu:
English Premier Laraba 1 ga watan Janairu
- Brentford da Arsenal
English Premier Asabar 4 ga watan Janairu
- Brighton da Arsenal
English League Cup Talata 7ga watan Janairu
- Arsenal da Newcastle
English FA Cup Lahadi 12 ga watan Janairu
- Arsenal da Man Utd
English Premier Laraba 15 ga watan Janairu
- Arsenal da Tottenham
English Premier Asabar 18 ga watan Janairu
- Arsenal da Aston Villa
Champions League Laraba 22 ga watan Janairu
- Arsenal da Dinamo Zagreb
English Premier Asabar 25 ga watan Janairu
- Wolves da Arsenal
Champions League Laraba 29 ga watan Janairu
- Girona da Arsenal