‘Mauludi nuna godiya ne ga babbar kyautar da Allah ya yi wa duniya’
Al’ummar Musulmi a faɗin duniya na bikin zagayowar Ranar Haihuwar Annabi Muhammadu (S.A.W) wadda akasari ke yi a rana mai kamar ta yau 12 ga watan Rabi’ul Awwal wadda a bana ta zo daidai da 15 ga watan Satumban 2024.
Malamai na cewa shi ne Fiyayyen Halitta kuma Annabi Ƙarshe a jerin manzonnin da Allah ya aiko wa duniya domin su zama haske sannan su jagoranci al’umma zuwa shiriya.
Albarkacin zagayowar wannan rana, BBC ta zanta da Sheikh Halliru Maraya, wanda ya yi mana bayani a kan muhimmancin bikin Mauludi.
Malamin ya ƙara da cewa bikin Mauludi, manuniya ce ta girmama Ma’aikin Allah da nuna soyayya a gare shi.
A cewarsa, masu bikin Mauludi na kuma nuna godiya a kan babbar kyautar da Allah ya yi wa al’ummar duniya ta aiko Fiyayyen Halitta don ya jagorance su zuwa ga hanya madaidaiciya.
Sheikh Halliru Maraya ya ce ana iya yin bikin Mauludi kuma ta hanyar yin girke-girke a raba abincin kyauta ga jama’a. Sannan a kai ziyara domin sada zumunci ga ƴan’uwa da abokan arziƙi, a ziyarci wurare kamar asibiti don gayar da marasa lafiya, da gidajen yari don ganin halin ɗaurarru suke ciki kuma a kai musu abinci da kayan masarufi da tufafi, a shaida musu cewa an yi musu ne albarkacin zagayowar Ranar Haihuwar Annabi.



