Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Real ta yi wasa na 45 a jere ba a doke ta ba a dukkan karawa
Real Madrid ta doke Deportivo Alaves 5-0 a wasan mako na 36 a La Liga da suka kara ranar Talata a Santiago Bernabeu.
Minti 10 da take leda Jude Bellingham ya fara zura kwallo, sannan Vinicius Junior ya ci na biyu da kuma Federico Valverde ya zura na uku a raga.
Saura minti 20 a tashi wasan Vinicius Junior ya kara kwallo na hudu kuma na biyu da ya ci a fafatawar, sai kuma Arda Guler ya zura na biyar a raga.
Wannan shi ne wasa na biyu da suka kara a bana a gasar, bayan da Real Madrid ta je ta ci 1-0 ranar 21 ga watan Disambar 2023, inda Lucas Vazquez ya ci kwallon.
Da wannan sakamakon Real tana ta daya da maki 93, wadda tuni ta lashe La Liga na bana, kuma saura wasa bibiyu ya rage a kare kakar bana.
Kuma Real ta yi wasa 45 a jere ba tare da an doke ta ba, wadda rabon da ta yi rashin nasara tun 3-0 da Atletico Madrid ta ci ranar 24 ga watan Satumba.
A karshen mako Real Madrid ta yi bikin lashe La Liga na bana na 36 jimilla, wadda ta dauki kofin tun kan kammala gasar nan.
Yanzu abinda ke gaban kungiyar da Carlo Ancelotti ke jan ragama shi ne wasan karshe a Champions League da Borussia Dortmund ranar 1 ga watan Yuni a Wembley.
Real Madrid mai Champions League 14 jimilla ta kai wannan matakin bayan da ta yi waje da Bayern Munich.
Ita kuwa Dortmund, wadda take da kofin zakarun Turai daya, za ta buga wasan karshe a Champions League karo na uku a tarihi.
Ƙungiyar Jamus ta kai wasan karshe ne, bayan da ta yi waje da Paris St Germain da cin 2-0 a karawa gida da waje a gasar.
Ƴan wasan Real Madrid da suka fuskanci Alaves ranar Talata:
Mai tsaron raga: Courtois, Lunin da kuma Kepa.
Mai tsaron baya: Carvajal, Militão, Nacho, Lucas Vázquez, Fran García, Rüdiger da kuma Mendy.
Masu buga tsakiya: Bellingham, Kroos, Modrić, Camavinga, Valverde, Ceballos, Arda Güler da kuma Mario Martín.
Masu cin kwallaye: Vini Jr., Rodrygo, Joselu da kuma Brahim.