Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Da alama sabuwar baraka na shirin kunno kai a jam’iyyar PDP
Ga alama daukar gwamnan Jihar Delta, Ifeanyi Okowa, da dan takarar shugaban kasa a babbar jam’iyyar adawa a Najeriya PDP Atiku Abubakar ya yi na nuna yiwuwar barkewar sabuwar baraka a jam`iyyar.
Irin yadda wasu fitattu a jam’iyyar da ake yi wa kallon manya a PDP suka fito suna kokarin kwayewa dan takarar shugaban kasar zani a kasuwa, inda suke cewa bai kyauta ba da ya tsallake gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike, ya dauki a matsayin abokin takara, alama ce ta yankan shakku cewa za su kunna wata wutar rikici, wadda idan ba a yiwu tubkar-hanci ba za ta cinye jam`iyyar.
Farfesa Kamilu Sani Fagge, Malami a Jami`ar Bayero ta Kano, ya shaida wa BBC cewa idan jam’iyyar ta PDP ba ta yi kokari ta dinke barakar da ke cikinta ba, hakan zai yi mata babbar illa.
Ya ce “Irin wannan barakar ce ta janyo wa jam’iyyar matsala a zaben 2015, don haka idan har ba su dinke ta ba lallai za su sha mamaki a zabe mai zuwa.”
Shi dai gwamnan jihar Binuwai Samuel Ortom, a wata zantawa da`yan jarida ya ce sam-sam dan takarar shugaban kasar Atiku Ababukar, bai yi halacci ba da ya ki amincewa da gwamna Wike a matsayin mataimaki.
Ya kuma ce ko bayan da ya zabi Okowa, bai yi wani yunkurin lallashin Wike ba, don haka babu laifi idan Wike ya juya wa jam`iyyar da kuma dan takarar nasu baya.
Shi kuwa tsohon gwamnan Ekiti, Ayo Fayose, cewa ya yi a kule yake kuma ya yanke shawarar goyon bayan mulki ya koma kudancin Najeriya, wato yankinsa, saboda ba a kai ruwa daji gida bai jika ba.
Wadannan jiga-jigan PDP na wannan tada-kurar ne a dai-dai lokacin da wasu`yan takarar shugaban kasa da kusoshin wasu jam`iyyun hamayyar ke jele zuwa wajen Wike, kuma ga dukkan alamu da nufin yin wuf da shi daga jam`iyyar PDP.
Jam`iyyar PDP dai ba ta dade da kashe maganar karba-karba da tsayar da dan takarar shugaban kasa ba kuma sai ga wata sabuwa.