Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Man Utd na son Olise, Da wuya Arteta ya dawo da Tierney
Manchester United na son sayen ɗan wasan tsakiya na Crystal Palace Michael Olise, na Faransa kuma za ta iya musaya da ɗan bayanta Aaron Wan-Bissaka, a cinikin (Star)
Bisa ga dukkan alamu ba lalle ba ne kociyan Arsenal Mikel Arteta ya dawo da ɗan bayansa na Scotland Kieran Tierney, daga aron da yake a Real Sociedad a Janairun nan. (Football Insider)
Ɗan wasan tsakiya na Ingila Jordan Henderson, na matuƙar son komawa gasar Premier daga Al Ettifaq ta Saudiyya kuma zai ɗauki duk wani tayi da za a yi masa a wannan wata da muhimmanci. (Mail)
Ana sa ran Conor Gallagher ya ci gaba da zama a Chelsea a watan nan duk da sha'awar ɗan wasan na tsakiya na Ingila da Tottenham ke yi. (Mirror)
Mai yuwuwa Chelsea ta nemi Henderson, din, lamarin da zai iya sa Gallagher ya tafi. (football.london)
Wolves na duba yuwuwar karɓo aron wasu 'ƴan wasa a watan nan na Janairu, kuma ɗan gaban West Ham Danny Ings, ɗan Ingila na daga cikin waɗanda take hari. (Telegraph)
Everton na neman yi wa Sevilla yankan baya wajen karɓar aron matashin matashin ɗan wasan tsakiya na Tunisia Hannibal Mejbri daga Manchester United. (Fabrizio Romano)
West Ham na nazarin sayen ɗan gaba na gefe na Ajax da Netherlands Steven Bergwijn. (Sun)
Manchester City za ta iya bari har zuwa lokacin bazara kafin ta nemi sayen ɗan wasan tsakiya na Bayern Munich da Jamus Joshua Kimmich, domin ta same shi a farashi mai sauƙi. (Mirror)
Har yanzu tauraron ɗan wasan tsakiya na Manchester City Kevin de Bruyne, na Belgium shi ne ƙungiyoyin Saudiyya suka fi hari a lokacin kasuwar bazara. (Football Insider)
Juventus na ƙoƙarin cimma yarjejeniya da ɗan bayan Lille Tiago Djalo, na Portugal wanda Inter Milan ma na sonshi. (Fabrizio Romano)
Har yanzu Bayern Munich ba ta haƙura da zawarcin ɗan bayan Barcelona da Uruguay ba Ronald Araujo duk da cewa ba lalle ba ne Barca ta yarda ta sayar da shi a watan nan na Janairu. (Sky Sports)