Real Betis za ta ɗauki aron Antony na Man United

Asalin hoton, Getty Images
Real Betis tana jerin masu zawarcin ɗan wasan Manchester United, Antony, domin buga mata wasannin aro zuwa karshen kakar bana.
Ɗan wasan tawagar Brazil ya kasa nuna kansa a Old Trafford, wadda ta saye shi a matakin na biyu mafi tsada a tarihin ƙungiyar
United ta ɗauki ɗan ƙwallon kan £81.3m a Agustan 2022. Kawo yanzu ƙwallo 12 ya zura a raga har da uku da ya ci a wasa uku da ya fara buga Premier League.
Rabonda mai shekara 24 ya zura ƙwallo a raga tun Afirilun 2023 - hakan ya sa ba a saka shi a wasanni sosai, wanda ya kara buga wasa 22, sai ya aka sa shi wasa 15 a bara.
Antony ya buga wa United karawa 13 daga 32 a dukkan fafatawa a kakar bana.
Ƙungiyoyi da dama na son ɗaukar aron Antony, amma Unitede ta bukaci a biya wani kaso na albashin ɗan ƙwallon.
Ana sa ran Betis, wadda take ta 11 a teburin La Liga, mai fatan buga wasan cike gurbin Conference League da Gent, za ta ɗauki Antony, amma har yanzu ba a cimma matsaya ba.








