Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Man United ta kusan kammala ɗaukar Dorgu daga Lecce
Manchester United ta kusan kammala ɗaukar ɗan wasan Lecce, Patrick Dorgu a Janairun nan.
Tun bayan da Ruben Amorim ya karɓi aikin horar da United a cikin watan Nuwamba, ya ci karo da koma baya a ƙungiyar, musamman ƙarancin mai buga baya daga gefen hagu.
Hakan ya sa United ke fatan sayen Dorgu mai shekara 20, wanda ke daf da zama na farko da Amorim zai ɗauka a ƙungiyar.
Ana cewa kuɗin cinikin ɗan wasan zai kai £25.1m da karin kuɗin tsarabe-tsarabe da zai kai £4.2.
Ana sa ran Dorgu zai kammala ƙulla yarjejeniya da United ranar Laraba, yayin da kungiyar Old Trafford za ta buga wasan karshe a Europa League da FCSB ranar Alhamis.
Tun farko Amorim ya yi fatan sayen karin ƴan wasa a watan Janairu, amma dokar kashe ƙudi daidai samu ta sa ya samu tsaiko.
United ta bayar da aron Antony ga Real Betis, domin buga babbar gasar tamaula ta Sifaniya zuwa karshen kakar nan.
Ƙungiyar Sifaniya za ta biya kaso 84 cikin 100 na albashin ɗan wasan tare da karin ladan wasanni ba tare da yarjejeniyar sayar da ɗan wasan Brazil ba.
Marcus Rashford da Casemiro da Alejandro Garnacho suna daga cikin waɗanda makomarsu ba tabbas a United.