Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
West Ham ta ɗauki aron Todibo daga Nice
West Ham United ta kammala ɗaukar aron mai tsaron bayan Nice, Jean-Clair Todibo da yarjejeniyar sayen shi £34.22m a 2025, idan ya taka rawar gani.
Ƙungiyar da Julen Lopetegui ke jan ragama ta samu damar ɗaukar ɗan wasan mai shekara 24, bayan da Juventus ta yi zawarcinsa, wanda ya buga wa Faransa fafatawa biyu.
BBC ta fahimci cewar West Ham ta amince za ta sayi ɗan ƙwallon Manchester United, Aaron Wan-Bissaka domin ta kara karfin gurbin masu tsare baya.
Mai shekara 26, wanda ba zai buga wa United Community Shield ba, zai je West Ham a auna koshin lafiyarsa ranar Lahadi daga nan ya rattaba hannu.
Manchester United da Manchester City za su kara a Community Shield ranar Asabar a Wembley.
Todibo ya fara taka leda a Toulouse daga nan ya je Barcelona a 2019 daga nan ya buga wasannin aro a Schalke da Benfica, sai kuma Nice ta mallake shi.
Ɗan kasar Faransa, shi ne na shida da West Ham ta ɗauka kan fara kakar nan, tun bayan da David Moyes ya ajiye aikin a karshen kakar da ta wuce.
Ƙungiyar ta kashe £100m wajen sayen Crysencio Summerville daga Leeds da Niclas Fullkrug daga Borussia Dortmund da Luis Guilherme daga Palmeiras da Max Kilman daga Wolves da kuma Guido Rodriguez.
West Ham za ta fara wasan farko a 2024-25 a Premier League da fuskantar Aston Villa ranar 17 ga watan Agusta.