Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Lupus: Cutar garkuwar jiki da ake gano ƙarin masu fama da ita a Najeriya
A shekarun baya-bayan nan, ana gano ƙarin mutanen da ke fama da cutar lupus a Najeriya.
Ƙwararru a fannin lafiya kamar Dr. Maryam Ahmed, likitar gaɓoɓin jiki a Asibitin Koyarwa na Jami'ar Ahmadu Bello Zariya, na cewa duk da yake ana gano ƙarin masu cutar amma ba lallai ne a ce tana ƙara yawa ba.
Hukumomin lafiya a duniya sun keɓe duk ranar 10 ga watan Mayun kowacce shekara domin tunawa da masu fama da lupus.
Lupus cuta ce wadda garkuwar jikin mutum maimakon ta yi aikinta na kare jiki daga miyagun ƙwayoyin cutuka, amma cikin kuskure sai ta juya ta riƙa nakasa lafiyayyun ƙwayoyin halittun jiki.
Masu cutar lupus kan yi fama da tsananin mutuwar jiki da yawan larurori sanadin alamomin cutar a sassan jiki.
Ƙwararru dai sun ce har yanzu ba a iya gano takamaimai abin da ke haddasa cutar lupus ba.
Sai dai, sun ce mai yiwuwa tana da nasaba da ƙwayoyin halittun gado kuma tana addabar sassan jikin da suka fi fitowa cikin hasken rana kamar; kai da fuska da hannuwa da fatar jiki.
Kalli bidiyon da ke sama domin ganin likita Maryam Ahmed da ƙarin bayani game da cutar lupus.