Stephanie Frappart ce za ta hura wasan Real Madrid da Celtic

Stéphanie Frappart

Asalin hoton, Real Madrid

An wallafa

Stephanie Frappart ce za ta yi alkalancin wasan Real Madrid da Celtic a Champions League ranar Laraba a Santiago Bernabeu.

Wannan shi ne karon farko da Frappart 'yar kasar Faransa za ta hura karawar da ta kunshi wasan Real Madrid a tarihi.

Celtic ta ziyarci Real Madrid domin buga wasa na shida a rukuni na shida a babbar gasar tamaula ta Zakarun Turai.

Ranar 6 ga watan Satumba Real Madrid ta doke Celtic 3-0 a wasan farko a cikin rukuni a Scotland.

Wannan shi ne wasa na hudu da za su kara a tsakaninsu, inda Real Madrid ta yi nasara a biyu, Celtic ta ci wasa daya.

Real Madrid mai maki 10 ita ce ta daya a rukuni na shida, sai RB Leipzig mai maki tara da Shakhtar Donesk mai shida da Celtic ta karshe mai biyu.

Daya wasan rukuni na shida za a buga tsakanin Shakhtar da Leipzig.

Tuni Real Madrid mai rike da kofin bara na 14 jumulla ta kai zagayen gaba, wannan karawar zai ba ta damar ci gaba da jan ragamr rukunin.

Frappart na cikin alkalan hukumar kwallon kafa ta duniya tun 2009 ta kuma ja ragamar manyan wasannin tamaula a duniya.