Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Watakila Lewandowski ba zai kara da Real ba ranar Alhamis
Watakila Robert Lewandowski ba zai buga wasan farko na daf da karshe a Copa del Rey da Barcelona za ta ziyarci Real Madrid ranar Alhamis ba.
Kungiyar ta Camp Nou ta sanar ranar Litinin a shafinta na Intanet cewar Lewandowski zai yi jinya.
Ba a fayyace ranar da zai koma taka leda da, amma kungiyar za ta ci gaba da auna koshin lafiyarsa kafin karawar ta El Clasico ranar 2 ga watan Maris.
Tsohon dan wasan Bayern Munich, shine kan gaba a ci wa kungiyar kwallaye a bana, wanda ya zura 25 a raga a dukkan fafatawa 31, har da 15 a La Liga.
Raunin Lewandowski wani koma baya ne ga kungiyar da Xavi ke jan ragama, bayan da Almeria ta ci Barcelona 1-0 ranar Lahadi a La Liga.
Wasa na biyu kenan da aka ci kungiyar Camp Nou a La Liga a kakar nan, wadda ta barar da damar bai wa Real Madrid tazarar maki 10 tsakani.
Haka kuma Barcelona ta ci karo da cikas, bayan da Manchester United ta fitar da ita da cin 4-3 gida da waje a wasan neman shiga Europa League zagayen 'yan 16.
Barcelona za ta fara zuwa Santiago Bernabeu ranar 2 ga watan Maris, domin buga wasan farko na daf da karshe a Copa del Rel na bana.
Daga nan za ta fafata da Valencia da kuma Athletic Bilbao a gasar La Liga, sannan ta karbi bakuncin wasa na biyu a Copa del Rey da Real ranar 19 ga watan Maris a Camp Nou.
Cikin Janairu Barcelona ta ci Real 3-1 ta lashe Sifanish Super Cup a Saudi Arabia, kafin nan Real ce ta fara cin Barca 3-1 a kakar bana a La Liga a 2022.