Bazoum ya shaida mana matsalolin da yake ciki - Tawagar Ecowas

Bazoum ya shaida mana matsalolin da yake ciki - Tawagar Ecowas
An wallafa

Tawagar ƙungiyar Ecowas da ta ziyarci Jamhuriyar Nijar domin shiga tsakani ta ec ta samu ganawa da hamɓararren shugaban ƙasar Mohamed Bazoum.

Wakilan na Ecowas - ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban mulkin sojin Najeriya janar Abduslami Abubakar mai ritaya - sun ce sun tattauna da Bazoum ya kuma shaida musu irin matsaloli da yake ciki.

Abdulsalami Abubakar ya ce za su shaida wa ƙungiyar Ecowas saƙon Bazoum da zarar sun koma.

Ya ƙara da cewa an samu mabuɗin tattaunawa tsakanin sojojin da suka yi juyin mulkin da kuma ƙungiyar Ecowas.