Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wasannin da suke gaban Arsenal zuwa karshen kakar bana
Kofi biyu ne suka rage da Arsenal ke fatan dauka a bana da ya hada da Premier League da kuma Champions League kafin kammala kakar 2023/24.
Saura wasa tara ya rage a karkare wasannin Premier League na bana, inda Arsenal take matakin farko da maki 64, iri daya da na Liverpool ta biyu.
Mai rike da kofin bara, Manchester City tana matsayi na uku a teburin da tazarar maki daya tsakaninta da Liverpool da kuma Gunners.
Sai dai Arsenal da Liverpool da kuma City kowacce wasa 28 suka buga a Premier, bayan da aka fafata a FA Cup a karshen mako.
Tuni Manchester City ta kai daf da karshe a FA Cup, bayan cin Newcastle United, ita kuwa Liverpool ta yi ban kwana da gasar, sakamakon da Manchester United ta doke ta 4-3.
Tun farko sun tashi 2-2 a Old Trafford ranar Lahadi daga nan suka shiga karin lokaci, inda kungiyar da Erik ten Hag ke jan ragama ta kai zagayen daf da karshe.
A watan gobe ne United za ta kece raini da Coventry City mai buga Championship a daf da karshe a FA Cup a Wembley na bana.
Ita kuwa City mai kofin bara na bakwai jimilla za ta buga wasan hamayya da Chelsea a watan goben a Wembley a zagayen daf da karshe.
An fitar da Arsenal a League Cup ranar Laraba 1 ga watan Nuwamba, bayan da West Ham United ta yi nasarar cn 3-1.
Haka kuma Liverpool ce ta yi waje da Gunners a FA Cup na kakar nan ranar 7 ga watan Janaiiru, bayan da aka ci Arsenal 2-0 a Emirates.
A gasar Premier League, Gunners mai wasa 28 ta yi nasarar cin 20 da canjaras hudu aka doke ta fafatawa hudu da cin kwallo 70 aka zura mata 24 a raga mai maki 64.
Wadanda suke kan gaba a cin kwallaye a Premier League
Erling Haaland Manchester City 18
Ollie Watkins Aston Villa 16
Mohamed Salah Liverpool 15
Dominic Solanke Bournemouth 15
Heung-min Son Tottenham 14
Jarrod Bowen West Ham United 12
Bukayo Saka Arsenal 13
Alexander Isak Newcastle United 12
Phil Foden Manchester City 11
Cole Palmer Chelsea 11
Wasannin mako na 30 a Premier League
Ranar Asabar 30 ga watan Maris
- Newcastle United da West Ham
- Chelsea da Burnley
- Tottenham da Luton Town
- Nottingham Forest da Crystal Palace
- Sheffield United da Fulham
- Bournemouth da Everton
- Aston Villa da Wolverhampton Wanderers
- Brentford da Manchester United
Ranar Lahadi 31 ga watan Maris
- Liverpool da Brighton & Hove Albion
- Manchester City da Arsenal
Wasannin da suka rage a gaban Arsenal
Saura wasa tara Arsenal za ta buga a Premier League kafin karkare kakar bana da fafatawa biyu a Champions League.
Cikin watan Afirilu Gunners za ta kara da Bayern Munich gida da waje a babbar gasar zakarun Turai ta bana, zagayen kwata fainals.
Idan har Arsenal ta yi nasarar kai wa zagayen gaba, kenan tana da sauran wasa uku a gabanta da ya hada da na daf da karshe gida da da waje da kuma wasan karshe.
Haka kuma tana da kwantan wasa daya kenan a Premier League da ya kamata ta kara da Chelsea ranar 16 ga watan Maris.
An dage fafatawar, sakakon da Chelsea ta buga wasa da Leicester City a FA Cup ta kuma kai zagayen daf da karshe za ta fuskanci Manchester City a watan gobe a Wembley.
Arsenal, wadda ta yi shekara 20 rabon ta dauki Premier League, ba ta taba lashe Champions League ba, wadda ta taba kaka 20 a jere tana zuwa gasar.
Wasannin da ke gaban Arsenal a yanzu haka
Premier League Ranar Lahadi 31ga watan Maris 2024
- Man City da Arsenal
Premier League Ranar Laraba 3 ga watan Afirilu 2024
- Arsenal da Luton
Premier League Ranar Asabar 6 ga watan Afirilu 2024
- Brighton da Arsenal
Champions League Ranar Talata 9 ga watan Afirilu 2024
- Arsenal da Bayern Munich
Premier League Ranar Lahadi 14 ga watan Afirilu 2024
- Arsenal da Aston Villa
Champions League Ranar Laraba 17 ga watan Afirilu 2024
- Bayern Munich da Arsenal
Premier League Ranar Asabar 20 ga watan Afirilu 2024
- Wolves da Arsenal
Premier League Ranar Asabar 27 ga watan Afirilu 2024
- Tottenham da Arsenal
Premier League Ranar Asabar 4 ga watan Mayu 2024
- Arsenal da Bournemouth
Premier League Ranar Asabar 11 ga watan Mayu 2024
- Man Utd da Arsenal
Premier League Ranar Lahadi 19 ga watan Mayu 2024
- Arsenal da Everton
Arsenal a Champions League
Arsenal ta kawo matakin kwata fainals a Champions League a bana, bayan da ta buga karawa takwas, wadda ta yi nasara biyar da canjaras daya da rashin nasara biyu.
Kungiyar da ke Emirates ta ci kwallo 17 aka zura mata biyar a raga, wadda ta yi nasara a kan FC Porto a zagayen 'yan 16 a gasar ta zakarun Turai.
Kenan Gunners ta kai kwata fainals a Champions League a karon farko tun 2009/10.
Sannan ta kawo karshen rashin nasara bakwai a jere a zagayen 'yan 16 a gasar ta zakarun Turai.
Arsenal ta taba jera kaka 20 tana buga Champions League, wadda ta kai wasan karshe daya daga ciki, amma ba ta taba lashe kofin ba.
Arsenal ta buga Champions League ko European Cup karo 209 da yin nasara 106 da canjaras 44 da rashin nasara 59 ta zura kwallo 349 aka zura mata 223 a raga.