Champions League: Madrid za ta kara da Man City, Arsenal da Munich

An wallafa

Arsenal za ta kece raini da Bayern Munich yayin da Manchester City kuma za ta buga da Real Madrid a zagayen kwata fainal na gasar zakarun Turai.

Arsenal ce za ta karɓi baƙuncin Bayern a filin wasa na Emirates a karawar fark, inda kyaftin ɗin Ingila Harry Kane zai koma birnin London.

Wannan ne karo uku jere da Manchester City ta kara da Real a matakin sili ɗaya ƙwale na gasar.

Za a yi karawar farkon ranar 9 zuwa 10 ga watan Afrilu inda karawa ta biyu kuma za a yi a ranar 16 zuwa 17 na watan Afrilu.

Jadawalin

Zagayen kwata fainal

  • Arsenal v Bayern Munich
  • Atletico Madrid v Dortmund
  • Paris St-Germain v Barcelona
  • Real Madrid v Manchester City

Zagayen kusa da ƙarshe

  • Atletico Madrid ko Borussia Dortmund v Paris St-Germain ko Barcelona
  • Arsenal ko Bayern Munich v Real Madrid ko Manchester City