Barca za ta ci gaba da sauya ƴan wasan a gasar da take yi - Flick

Hansi Flick

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Barcelona za ta ci gaba da sauya ƴan wasanta, bayan da za ta karɓi bakuncin Real Sociedad a gasar La Liga ranar Lahadi n ji koci, Hansi Flick.

Barcelona ta yi wasa 14 a jere da tare da rashin nasara ba a La Liga da Copa del Rey da kuma Champions League, mai fatan lashe kofi uku nan gaba.

Tun cikin watan Janairu Bacelona ta lashe Spanish Super Cup na bana a Saudi Arabia, bayan doke Real Madrid a wasan karshe.

''Ba abu ne mai sauki sauya ƴan wasan nan ba, kowa so yake ya bayar da gudunmuwarsa. Amma za mu ci gaba da anfani da su domin ci gaban ƙungiyar.'' in ji Flick

Barcelona za ta buga wasa huɗu cikin kwana 10 nan gaba, wadda za ta fara da fuskantar Sociedad a ranar Lahadi.

''Muna da kofi uku da muke fatan ɗauka nan gaba. Lokacin da muka fara kakar nan ba wanda ya ɗauk za muyi ƙwazo irin haka.''

''Akwai abubuwa da ke faruwa a kakar nan, ina canja yadda muke gudanar da atisaye,'' kamar yadda Flick ya sanar.

''A wasan Copa del Rey karawa da Valencia mun sa wasu ƴan wasan sun huta, kuma sun yi kokari sosai - ya kamata mu mayar da hankali kan fafatawar nan.

Ƙwallo 25 ya shiga ragar Barcelona har da 4-4 da ta tashi da Atletico Madrid a wasan farko a daf da karshe a Copa del Rey cikin Fabrairu.

Barcelona za ta yi wasan na ranar Lahadi ba tare da Andreas Christense ba, wanda ya kara yin rauni.

Christensen, mai shekara 28, bai fara kakar bana ba, sakamakon jinya, bayan da ya koma taka leda sai ya kara jin rauni a cikin Janairu.