Van Dijk bai gamsu da tayin Liverpool ba, Arsenal na son Cunha

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Liverpool ta miƙawa ɗan wasan baya ba ƙasar Netherlands Virgil Van Dijk sabon kwantiragi, amma ɗan wasan mai shekara 33 bai gamsu da tayin kulob ɗin ba. (Athletic)

Arsenal ta tuntuɓi Wolves kan yiwuwar ɗaukar ɗan wasan gaba na ƙasar Brazil Matheus Cunha mai shekara 25. (Caught Offside)

Makomar Julen Lopetegui a matsayin kocin West Ham tana tangal-tangal. (Sky Sports)

Edin Terzic da Roger Schmidt da Sergio Conceicao da Massimiliano Allegri da Graham Potter- waɗanda a halin yanzu ba su da ƙungiya - na ckin jerin sunayen da West Ham ke nazari a kai domin maye gurbin Lopetegui. (Telegraph)

Tsohon kocin Denmark Kasper Hjulmand shi ma yana ɗaya daga cikin masu horaswan da West Ham ke iya tuntuɓa idan har ta sallami Lopetgui. (Sky Sports Germany)

Dan wasan tsakiya na Sifaniya Rodri ya buƙaci Manchester City da ta yi zawarcin abokin wasansa na tawagar ƙasa kuma ɗan wasan gaba na Athletic Bilbao Nico Williams, mai shekara 22. (Metro)

Ɗan wasan baya na Ingila Harry Maguire, mai shekara 31, yana jan hankalin ƙungiyoyin Premier da dama sakamakon rashin tabbas kan makomarsa a Manchester United. (Football Insider)

Kocin Paris St-Germain Luis Enrique ba ya sha'awar kulob ɗin na Faransa ya ɗauko ɗan wasan gaba na Sporting da Sweden Viktor Gyokeres, mai shekara 26, wanda ke jan hankalin Manchester City da Manchester United. (Foot Mercato)

Newcastle United na sanya ido kan ɗan wasan Bournemouth da Ghana Antoine Semenyo, mai shekara 24, da kuma ɗan wasan Brentford da Kamaru Bryan Mbuemo, mai shekara 25. (The i News)

Arsenal da Liverpool na shirin gogayya kan ɗan wasan gaba na LA Galaxy da Brazil Gabriel Pec mai shekra 23.

Kungiyoyin Premier sun sanya ido kan halin da ɗan wasan gaban Celtic ɗan ƙasar Scotland Daniel Cummings mai shekaru 18 ke ciki. (Mail)