Fatan Amurkawa kan sabon shugaban ƙasa
Fatan Amurkawa kan sabon shugaban ƙasa
An wallafa
Yayin da Amurkawa ke kaɗa ƙuri'a a zaɓen shugaban ƙasa ranar Talata, da yawansu na fatan cigaba a rayuwarsu idan sabon shugaban ya kama mulki.
Masu sharhi na cewa wannan ne zaɓe mafi muhimmanci da tasiri a Amurka tsawon lokaci.
'Yartakarar jam'iyyar Democrat kuma mataimakiyar shugaban ƙasa a yanzu, Kamala Harris na fafatawa da tsohon Shugaban Ƙasa Donald Trump na jam'iyyar Republican.



