Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An yi canjaras tsakanin Autan na Aisha da Dan Aliyun Arewa
An buga turmi uku ba kisa tsakanin Autan na Aisha da Dan Aliyun Arewa a Maraba a damben naira 100,000.
An yi wasan ne a safiyar Lahadi a gidan wasa na Idris Bambarewa da ke 'yan tifa a karamar hukumar Karo a Marabar 'Nyanya jihar Nasarawa, Najeriya.
Damben gasa ne da aka sa tsakanin Dan Aliyu dan wasan Arewa da Autan na Aisha dan damben Guramada.
Tun kan wasan sai da Labaran dan gwamba ya wake su, sannan 'yan kallo suka yi musu alherin kudi tun kan fara dambe.
Daga nan suka fara turmi na daya ba kisa, alkalin wasa Anas Dan Dume ya bukaci su hutu, sannan suka yi turmi na biyu da na uku duk ba a samu gwani ba.
Tun kafin nan an dambata tsakanin Fatalwar Shagon Alabo da Garkuwan Yahayan Tarasa, inda suka tashi canjaras.
Shi kuwa Bahagon Ali Yaro, buge Shagon Dan Aliyu ya yi, da wanda Bahagon Dan Shago ya yi nasara a kan Shagon Terminator.
Wasa tsakanin Dan Yalon Tula da Rabe Bahagon Ebola ya kayatar, amma turmi daya suka yi, bayan da Rabe ya fama ciwo a hannunsa.
An kuma yi wasan da bai yi kisa ba tsakanin Dogon Inda da Bahagon Yahaya, sai dai Ushu ya doke Shagon Basiru a wani sa zaren.
Damben Ilele da Garkuwan Yahayan Tarasa ya kayatar, amma turmi biyu suka yi ba kisa aka raba su, an karkare da wasan Dogon Maiduguri da Na Jimama, wanda ba kisa.