Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Liverpool ta sayar da Minamino ga Monaco
Liverpool ta amince ta sayar da dan kwallon tawagar Japan, Takumi Minamino ga Monaco kan fam miliyan 15.5.
Kungiyar da ke buga Ligue 1 tana daga jerin masu zawarcin dan wasan mai shekara 27, wanda ya koma Reds daga Red Bull Salzburg kan fam miliyan 7.25 a 2020.
Dan wasan ya ci kwallo 14 a wasa 55 da ya yi wa Liverpool, kuma shi ne kan gaba a zura kwallaye a raga a FA Cup da League a kakar da aka kammala.
Kwallo bakwai da Minamino ya ci a kakar da ta wuce sun taimakawa Jurgen Klopp daukar FA Cup da League Cup.
Sai dai kuma wasa 11 ya yi a kakar da ta wuce da Liverpool ta yi ta biyu a Premier League, kofin da Manchester City ta lashe.
Minamino ya buga wasannin aro a Southampton a Fabrairun 2021 da yin wasa 10, daga baya ya koma Liverpool a kakar 2021-22.
Tuni dai Sadio Mane ya kammala komawa Bayern Munich, kan kwantiragin kaka uku.
Bayan da dan wasan tawagar Senegal ya koma Bundesliga, Liverpool ta dauko dan kwallon tawagar Uruguay, Darwin Nunez daga Benfica kan fam miliyan 64.
Haka kuma Liverpool ta dauki Fabio Carvalho daga Fulham kan fam miliyan biyar da kuma matashin dan wasa mai shekara 18, Calvin Ramsay daga Aberdeen kan fam miliyan 4.2.