Muller ya yi ritaya daga buga wa Jamus tamaula

Asalin hoton, Getty Images
Thomas Muller ya sanar da yin ritaya daga buga wa tawagar Jamus tamaula, bayan kammala gasar cin kofin nahiyar Turai ta Euro 2024.
Ya rataye takalmansa bayan wasa 131 da cin ƙwallo 45 a tawagar Jamus, wadda Sifaniya ta fitar da ita a Euro 2024, duk da ita ta karɓi bakuncin wasannin.
Mai taka leda a Bayern Munich, shi ne na uku a yawan yi wa Jamus wasanni, bayan Miroslav Klose mai 137 da kuma Lothar Matthaus mai 150.
Muller ya fara buga wa Jamus wasan sada zumunta da Argentina a 2010, wanda ya yi wa tawagar gasar cin kofin duniya a shekarar da cin ƙwallo biyar da lashe ƙyautar takalmin zinare a gasar.
Yin ritaya da Muller ya yi na nufin koci, Julian Nagelsmann ya rasa fitattun ƴan wasa a tawagar, bayan da Toni Kross shima ya daina buga tamaula a Jamus da ƙungiya.
Haka kuma ana tantama kan makomar mai tsaron raga, Manuel Neur, mai shekara 38, wanda shi ne na biyar a yawan buga wa Jamus tamuala mai wasa 124.
Sifaniya ce ta fitar da Jamus a zagayen daf da karshe a gasar cin kofin nahiyar Turai ta Euro 2024.
Kawo yanzu Sifaniya ta zama kan gaba a yawan lashe Euro mai huɗu jimilla, sai Jamus mai uku da Italiya da Faransa masu bibiyu.










