Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Chelsea ta kammala daukar Mudryk daga Shakhtar Donetsk
Chelsea ta kammala daukar dan kwallon tawagar Ukraine, Mykhailo Mudryk daga Shakhtar Donetsk.
Mai shekara 22 ya amince da kunshin kwantiragin kaka takwas da rabi a Stamford Bridge
Kungiyar Stamford Bridge ta dauki dan wasan kan fam miliyan 62 da karin tsarabe-tsarabe na fam miliyan 27.
Chelsea ta dauki Mudryk dan wasan da Arsenal ta yi fatan saya, wanda ya ci kwallo bakwai a wasa 12 da ya yi a lik a Shakhtar a kakar nan.
Shi ne dan kwallo na biyar da Chelsea ta dauka a lokacin cinikayyar 'yan wasan tamaula a watan Janairu.
Mudryk, wanda ya buga wa Ukraine wasa takwas tun bayan da ya fara yi mata tamaula a Yunin 2022 ya halarci Stamford a wasan Chelsea da Crystal Palace a gasar Premier League ranar Lahadi.
Bayan Mudryk da Chelsea ta dauka na biyar a Janairu, sauran sun hada da Jaox Feliv da ta dauka aro daga Atletico Madrid ta kuma biya kudin Benoit Badiashile da David Datro Fofana da kuma Andrey Santos.
Kawo yanzu Chelsea ta kashe sama da fam miliyan 400 wajen saye 'yan wasa tun bayan da attajiran da suka sayi kungiyar daga Amurka, karkashin jagorancin Todd Boehly a Mayun 2022.