Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Garin da ya fi kowanne iska mafi kyawu da daɗi a duniya
Daga Anna Filipova
BBC Future
Iskar da ke kaɗawa kusa da ni, tana tayar da ƙura mai kama da zinare a duk lokacin da mutum ya yi numfashi.
Wajen na da sanyi a saman wannan tsauni, tsakiyar wani wuri da a can baya yake hamada mai ƙanƙara.
Busasshiyar iska da ke kaɗawa, na sanya ɗumi a bakina da kuma hanci da ke fitar da ƙanƙara.
Ina tsaye kusa da tsaunin Zeppelinfjellet, mai nisan kilomita 556 a Brøggerhalvøya da ke yankin Spitsbergen a Svalbard, da ke arewacin tekun Arctic.
A kasan tsaunin, wani ƙaramin gari ne mai suna Ny-Alesund da ke da al’ummomi da ba su fi 45 ba lokacin hunturu sannan kusan 150 a lokacin bazara.
Gari ne dake arewacin duniya inda mutane ke rayuwa.
Tsaunin dai ya fi girma ta gefe daya, inda daya ya fi daya, wuri ne mai kyawun gaske.
Tsaunin na daya daga cikin wurare mafi kyau da mutum zai yi numfashi – wurin kuma yana da nisan gaske daga ababen da za su janyo gurbacewar muhalli, iskar da ke kadawa a nan, na daga cikin mafi kyau a duniya.
Yawancin mazauna garin masana ne wadanda suka zo don yin bincike.
A 1989, an ƙirƙiro wata cibiyar bincike a iyakar Zeppelinfjellet da ke tsawon mita 472, domin taimaka wa masu bincike sanya ido kan abin da zai kawo gurɓatar muhalli.
A baya-bayan nan ana kiran tashar da suna Zeppelin, inda ta zamanto wani wuri mai muhammanci na auna wurare da ke gurbata muhalli da kuma ke kawo sauyin yanayi.
Amma akwai alamomi da ke nuna cewa iska mai kyau a wajen na canzawa. So tari, tashoshi na fitar da gurbatacciyar iska daga nahiyar Turai da arewacin Amurka zuwa wannan yankin na Svalbard.
Ba alama ta barazana ga muhalli kadai masana suka hango ba, har ma da alamomin sabbin abubuwa da ke gurbata muhalli da ke iska ke janyowa wadanda kuma ke kara sanya masanan cikin damuwa.
Binciken da ake a Ny-Alesund, wani bangare ne na kokarin da ake yi a duniya domin ganin tasirin dan adam kan muhalli.
Matakai da suke dauka za su taimaka wajen gano gurbacewar muhalli da matsayinsa a duniya,’’ a cewar Hermansen.
Wani masani daga wata cibiya, ya lura cewa cikin kwanaki biyar a mako, na daukar nau’kan iska da kuma canza abubuwan aunawar.
Duba da yanayin wurin da kuma tsawonsa da kan iya gano iska da ta gurbace daga garin.
Cibiyar ta Zeppelin, wuri ne da ke taimaka wa wajen gano abin da ke faruwa na yanayi.
Ba tashoshin da ke gurbata muhalli ne kawai ba masanan suka duba, har ma da wasu sinadarai da ke kawo gurbacewar muhalli.
Wasu tashoshin bincike na kasa da kasa, sun yi amfani da alkaluma da masanan suka karba wajen yin duba kan ainihin ababen da ke gurbata muhalli.
"Duba da muka yi a nan ya kunshi abubuwa da dama,’’ a cewar Hermansen, da ya dauki kusan shekara ashirin yana aiki a cibiyar ta Zeppelin.
"Abubuwan da ke gurbata muhalli, abu ne da yake son duba saboda yadda yake shafar muhalli, yayin da auna tashoshi da ke fitar da gurbatacciyar iska, suma ke da muhimmanci a duniya saboda tasiri da suke yi wajen kawo sauyin yanayi a duniya.’’
Amma cibiyar Zeppelin za ta iya taimaka wa wajen yin gargadi kan saunyi da ake samu a cikin muhalli.
Alal misali, sinadarin methane a iskar da ke Zeppelin, ta kasance tana ƙaruwa tun 2005, inda ta kai mataki na sama a 2019.
A yanzu ana kara nuna damuwa kan irin gurbatacciyar iska da ke fita, da cewa na barazana ga dumamar yanayi a duniya zuwa ga 1.5 na ma’aunin Celsius.
Kwanaki goma bayan hadarin tashar nukiliya ta Fukushima a 2011, an gano wasu sinadarai da tashar ke fitarwa a Zeppelinfjellet.
An bayyana cewa, an gano wadannan sinadarai ne kwanaki kadan daga dubban kilomitoci.
Masu binciken a cibiyar Zeppelin, sun kuma ga karuwar wasu sinadarai a iska kusa da garin Ny-Alesund lokacin watannin bazara saboda karuwar jiragen ruwa na dakon kaya da ke zuwa yankin.
Masanan sun kuma gano karuwar sinadaran atom masu lahani tsakanin watan Maris da kuma Mayun kowani shekara a daidai lokacin da yanayi ke daukar gurbataccen iska daga Turai zuwa Asia.
Alal misali, yayin da kura ke tashi, tana kawo irin wani sauyi na sinadarai.
Gurbatacciyar iska da masana’antu ke fitarwa a Rasha, na kawo saunyi a iska lokacin da take kadawa zuwa wani wuri lokacin hunturu.
An kuma ga raguwar wasu manyan sinadarai kamar na lead da Mercury saboda tsaurara matakai kan kona shara na masana’antu.
Kokarin da ake wajen rage amfani da abubuwa – da za su iya zuwa iska idan aka watsa su – sun kawo raguwar abubuwa da wadannan sinadarai suke kawowa.
A baya-bayan nan, masu bincike sun lura da karuwar dutsar kankara a yankunan, inda ake kyautata zaton cewa hakan ya faru ne saboda iska.
Hakan ya sanya masu bincike a tashar Zeppelin saka ido a muhallin da kuma dutsar kankara da ke zuba a can.
Duk da gurbatacciyar iska da ke fitowa daga sassan duniya zuwa yankin, yana da nisan gaske daga gurbatacciyar iska da mutane ke fitarwa a muhalli.
Akwai wasu wurare da suma ke da iska mai kyau – a 2020, masu bincike sun gano iska mai kyau da ke fitowa daga kudancin tekun Antarctica zuwa kuma kudancin Australiya.
Sai dai, garin Ny-Alesund, na daya daga cikins wurare kalilan da mutane ke zuwa yin rayuwa na tsawon lokaci, ko da kuwa masanan yin bincike.
Sai dai, iskar bata kasance mai kyau haka ba a can baya.
Tsakanin 1916 zuwa 1962, gari ne da ake hakar kwal, kafin wani abin fashewa ya hallaka masu haka 21, wanda kuma ya janyo aka kwashe ‘yan yankin daga garin da kuma rufe da ake hakar kwal din.
Tun bayan nan, an sauya wajen zuwa inda ake fitar da alkaluma daga muhallin maimakon kwal.
"An yi ta aikin share wajen a-kai-a-kai tun bayan shekarun 1960, lokacin da aka rufe wajen hakar kwal din, amma akwai sauran abubuwan gurbata muhalli da aka bari a birnin,’’ a cewar Hanne Karin Tollan, wani mai bincike a garin Ny-Alesund, wanda wani kamfanin ma’aikatar kula da yanayi da muhalli da ake kira Bay AS, ke gudanarwa.
Kamfanin ya kuma gudanar da bincike domin gano gurbatacciyar iska a wajen a shekarar 2019-2022, don daukar matakai.
An aika dukkan shara zuwa wani wuri a Norway.
Sai dai, yayin da wadanda ke aiki a Ny-Alesund ke daukar yawancin lokaci domin duba abin da ke iska, rayuwa a garin abune da ba a saba da shi ba.
Mazauna garin sun fito ne daga kasashe daban-daban a duniya da suka hada da Faransa da Jamus da Birtaniya da Italiya da Norway da Japan da Kudancin Koriya da kuma China da sauransu.
Jirage daga garin Longyearbyen na Svalbard, na zuwa yankin ne sau biyu kadai mako.
Gine-gine a garin suna da tsawon mita 30 wadanda aka sanyawa sunaye na manyan biranen duniya: kamar Amsterdam da Landan da Mexico da kuma Italiya – da sauransu.
Sun kasance a matsayin wani tuni na ganin dangantakar diflomasiyya daga wurare daban a fadin duniya.
Cibiyoyin samar da intanet dai basu da yawa a garin – inda a yawan lokuta ake rufe wayoyin salula da kuma tsarin intanet na Wi-Fi.
Babu kuma nau’rorin aike da sakonni na rediyo wanda wani mataki ne na ganin garin ya kasance babu hayaniya, inda duk mai bincike da ke son amfani da wata hanyar sadarwa, sai ya nemi izini.
A lokuta da dama, tsawa na girgiza wasu bangarorin garin, inda da daddare, iska ke kadawa zuwa cikin gidajen mutane.
Yayin ziyara ta a garin, kowani yammaci, na kan sanya tufafi masu kare sanyi lokacin da na fita waje.
Yanayi, wani abune da ke sanya mutanen da ke aiki a garin cikin hadari.
A wasu lokuta yanayin sanyi na kai maki 37.2 na ma’aunin celcius lokacin hunturu. A watan Maris din wannan shekara – yayin wata ziyara da na yi zuwa garin Ny-Alesund – yanayi da aka samu a watan ya kai 5.5C(42F).
Rabon da a samu hakan tun shekarar 1976 inda aka samu 5.0C (41F).
A wasu lokuta ana samun yanayi da mutane ba su saba gani ba, inda ake samun tsawon lokaci na duhu ko kuma rana.
Na je zuwa wata cibiyar bincike ta kimiyya lokacin yanayi na zafi a shekarar, lokaci kuma da ake samun duhu na awa 24 ta tsawon watanni.
Idan ka je wurin dole ka yi amfani da tocila ko kuma hasken farin wata.
Wata matashin dalibi dan kasar Italiya da na hadu da shi, wanda kuma tafiya cikin duhu sau tari, yana gamuwa da iska da kuma zubar kankara.
Sai dai, duhun yana kuma nuna yanayi mai kyau na yanda haske ke tafiya a garin daga sararin samaniya.
Al’ummar garin na da wata dabi’a ta babu wanda zai rufe kofar duk wani gini saboda idan dabbobi suka bayyana, za a basu mafaka.
Akwai kuma wasu hadura bayan ta duhu da kuma sanyi da masu bincike ke yin duba a kai a wannan shekara.
Bayan tashi daga aiki da karfe 16:30, al’ummomin garin na zama a cikin gidajensu.
Garin na da wani wurin cin abinci daya inda mutane ke haduwa don yin mu’amala da juna lokacin cin abincin rana da kuma na dare, inda suke bayar da labarai tsakaninsu kan haske da ke fita a arewacin garin da kuma namun daji da suka yi karo da su.
Yawancin labaran da mutane ke bayarwa a junansu na kawo sauyi da ake gani a dan karamin garin.
Leif-Arild Hanjem, wanda ya yi aiki a matsyain injiniya ta tsawon shekaru a tashar bincike ta kasar Norway da ke garin Ny-Alesund, ya fada mani cewa yaje yankin ne tun shekarar 1984 kuma ya ga sauyi da dama a yankin.
A sararin samaniyar yankin Ny-Alesund, mazauna garin na ganin sauye-sauye da dama. Sai dai, har yanzu suna da ci gaba da shakar iska mafi kyawu daga yankin.