'Yan Man United da za su buga Gasar Cin Kofin Duniya a Qatar

Asalin hoton, Getty Images
Qatar za ta karbi bakuncin Gasar Cin Kofin Duniya da za a fara ranar 20 ga watan Nuwamba a kammala 18 ga watan Disambar 2022.
Ranar 14 ga watan Nuwamba ita ce ranar karshe da tawagogin da za su buga wasannin za su mika sunayen 'yan wasan da za su wakilce su.
Manchester United tana da tarin 'yan wasan da za su wakilce ta a Gasar Cin Kofin Duniya da za a fafata tsakanin kasashe 32.
Koda yake wasu kasashen ba su sanar da 'yan wasan da za ta je da su buga babbar gasar tamaula ta duniya ma kawo yanzu.
United za ta ziyarci Fulham domin buga wasan mako na 16 a gasar Premier League, daga nan za a yi hutu a babbar gasar tamaula ta Ingila sai bayan wasannin Qatar.
Jerin 'yan wasan United da za su buga Gasar Cin Kofin Duniya a Qatar:
Rukunin farko
- Qatar
- Ecuador
- Senegal
- Netherlands
Dan wasan United, Tyrel Malacia zai wakilci Netherlands.
Rukuni na biyu
- Ingila
- Iran
- Amurka
- Wales
'Yan wasan United a wannan rukunin daga Ingila suke
- Harry Maguire
- Luke Shaw
- Marcus Rashford
Rukuni na uku
- Argentina
- Saudi Arabia
- Mexico
- Poland
Lisandro Martinez zai wakilci Argentina mai taka leda a United
Rukuni na hudu

Asalin hoton, Getty Images
- Faransa
- Australia
- Denmark
- Tunisia
Denmark za ta je kofin duniya da Christian Eriksen mai wasa a United
Faransa za ta je da Raphael Varane, wanda ya ji rauni a wasan United da Chelsea
Tunisia za ta je da Hannibal Mejbri mai wasan aro a Birmingham daga United
Rukuni na biyar
- Spain
- Costa Rica
- Germany
- Japan
Ba dan wasan United a wannan rukunin, bayan da Sifaniya ba ta kira David de Gea ba mai wasa a Old Trafford.
Rukuni na shida
- Belgium
- Canada
- Morocco
- Croatia
Babu dan wasan United da zai buga kofin duniya a rukuni na shida
Rukuni na bakwai
- Brazil
- Serbia
- Switzerland
- Cameroon
'Yan wasa hudu daga United ne za su wakilci Brazil a Qatar
Casemiro
Fred
Antony
Alex Telles mai wasan aro a Sevilla daga United
Rukuni na takwas
- Portugal
- Ghana
- Uruguay
- Korea Republic
Kyaftin din Portugal, Cristiano Ronaldo daga United, wanda ake sa ran wannan ita ce gasa ta karshe da dan kwallon zai buga.

Asalin hoton, Getty Images











