Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Iyakar Lebanon: Dakarun Ireland da ke sa ido kan boyayyen rikicin Isra'ila
- Marubuci, Daga Nafiseh Kohnavard
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Persian
- An wallafa
Idan ka ji wata ƙara hakan yana nufin kana buƙatar gudu zuwa wurin da ke kusa," in ji Kyaftin Aódhan McGuinness yayin da muka isa sansanin Shamrock.
Shi ne daraktan tsara dabaru na rundunar sojojin Ireland da ke gudanar da wannan sansanin wanzar da zaman lafiya na Majalisar inkin Duniya kusa da kan iyakar Lebanon da Isra'ila.
Muna iya jin hayaniyar jirage maras matuki na Isra'ila da ke shawagi a sama. Ƙararsu na kamar busar da gashi ko reza na lantarki, kuma a halin yanzu suna zama dare da rana a garuruwa da ƙauyuka a kudancin Lebanon.
Wata fashewa mai ƙarfi a kusa ya katse bayanin da Kyaftin McGuinness yake kan dabarun kare kai.
"Eh, an fara zagayen na yau," in ji shi.
Fashewar wata alama ce yaɗuwar tashin hankali a yankin tun bayan da ƙungiyar Hamas ta kaddamar da harin da ba a taɓa gani ba a kan Isra'ila a cikin watan Oktoba.
Tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD, wadda aka fi sani da Unifil, ita ce ke da alhakin sanya ido kan iyakar da ta raba Isra'ila da Lebanon, wadda ba ta kan ka'ida.
A cikin shekaru arba'in da suka gabata yankin ya sha fama da tashe-tashen hankula tsakanin ƙungiyar mayaka ta Shi'a ta Lebanon, Hezbollah, da kuma sojojin Isra'ila.
Yayin da ƙasashen Birtaniya da Amurka da sauransu ke yi wa ƙungiyar Hezbollah lakabin ƙungiyar ta'addanci, jam'iyyar siyasa ce ta ƙasar Lebanon wadda ke jagorantar kawancen da ya gaza samun rinjaye a majalisar dokokin ƙasar a zaɓen da ya gabata.
Sanye da rigunan kariya, mun shiga cikin gungun dakarun wanzar da zaman lafiya ɗauke da makamai a cikin ayarin motoci masu sulke na tsawon mintuna 20, zuwa wani sansanin da ke da nisan mita 500 daga iyakar.
Yayin da ake iya ganin makaman sojojin Isra'ila a kan iyakokin ƙasar, kwamandan sansanin, Laftanar Dylan Cadogan, ya ce sau da yawa su kan fake a cikin shingaye lokacin hare-hare, wani lokacin na tsawon sa'o'i.
"Mun ga an ruguza gidaje kuma mun ga fararen hula da aka kama waɗanda ke buƙatar taimakonmu."
Daga wani shingen hangen nesa na sansanin, ya nuna wani gida mai ruwan hoda daga nesa: "Akwai wata uwa da yaro a cikin ginin da ke da nisan mita 400 daga inda muke.
"An ruguza gidan, kuma sun gudu zuwa nan domin mafaka, mun kuma ba su taimakon magani da ɗaukarsu zuwa wurin kariya."
Dakarun na Unifil sun gano gawawwakin mutanen da aka kashe a rikicin, sai dai ba za su iya bayyana yawan mayakan Hezbollah a ciki ba saboda yanayin aikinsu da kuma buƙatar zama ɗan ba-ruwana tsakanin ɓangarorin da ke faɗa da juna.
"Ba aikinmu ba ne na yin magana a kan waɗannan abubuwa, kawai mu sa ido, da kuma bayar da rahoton abin da muka gani ga hedkwatar mu," in ji Laftanar Cadogan.
Tun bayan da Isra'ila ta kaddamar da munanan hare-hare a kan Gaza bayan harin Hamas a ranar 7 ga Oktoba, Hezbollah ta sha kai harin roka da na jirage maras matuki akai akai daga kudancin Lebanon, inda wasu daga cikin hare-haren suka nufi kan shingayen sojoji, yayin da wasu kuma suka faɗa arewacin Isra'ila.
Sojojin Isra'ila sun mayar da martani ta hanyar kai kazaman hare-hare ta sama da na makaman atilari.
Sakamakon faɗan, an ɗaiɗaita mutum 60,000 daga yankin da ke iyaka da Lebanon, yayin da aka kwashe dubban Isra'ilawa daga arewacin ƙasar.
Ƙungiyoyi masu sa ido sun ce a makon farko na faɗan bayan harin Hamas a watan Oktoba, an samu rahoton kai hare-hare kusan 70 a iyakar Isra'ila da Lebanon, kuma ya zuwa tsakiyar watan Nuwamba, hare-haren sun ƙaru zuwa 250 a kowane mako.
An fara tura dakarun wanzar da zaman lafiya a 1978 bayan da Isra'ila ta mamaye kudancin Lebanon, a wani martani na hare-hare kan iyaka daga ƙungiyar fafutuka ta Falasɗinawa (PLO).
Tun bayan nan, sama da dakarun wanzar da zaman lafiya 300 ne aka kashe, 48 daga cikinsu sun kasance ƴan Ireland, abu kuma da ke cikin zukatan iyalan dakarun.
A lokacin da aka tura Kaftin Tony Smith, mai shekara 27, zuwa fagen daga karo na biyu, ya kasance yana yawan kwantar wa da ƴan uwansa da ke gida Wexford, a kudu maso gabashin Ireland hankali.
"Mahaifiyata na son na koma gida, wanda tabbas zan koma, sai dai ta san me ya kawo mu nan kuma duk da damuwa da take ciki, tana ba mu goyon baya.'
Tinkarar garin Tebnine, fostocin jagoran Hezbollah Sheikh Hassan Nasrallah da kuma mayakan ƙungiyar da suka kwanta dama ne ke jere a kan hanya.
Garin na nisan kilomita 10 ne da iyakar Isra'ila da Lebanon kuma an lalata shi a tashin hankali da ka fuskanta a baya.
Kamar yawancin garuruwa da kuma kauyuka a kudancin Lebanon, Hezbollah na da tasiri sosai a nan kuma suna iko da tsaro a yankin.
Ɗaya daga cikin mazauna yankin, Ali Saad mai shekara 57, ya ce ya girma da dakarun wanzar da zaman lafiya na Ireland.
Da yake magana da yaren ƙasar ta Ireland, Ali ya ce ɗaya daga cikin dakarun ya taimaka wajen koyar da shi Turanci lokacin da yake matashi.
Wannan sojan ya kasance ɗaya daga cikin mutane uku na dangin ƴan Ireland da suka yi aiki tare da jami'in Unifil.
Mahaifinsa ya yi aiki shekaru da yawa da suka wuce, kuma a halin yanzu ɗansa yana can a Lebanon.
Ali ya yaba wa sojojin Ireland da taimakon da suka yi wajen ceto rayuwarsa lokacin da suka ɗauke shi daga makaranta suka kai shi ɗaya daga cikin sansanoninsu yayin wani harin sama.
A cikin shekarun da suka gabata, ya yi aiki a matsayin mai fassara ga dakarun wanzar da zaman lafiya kuma gungun sojojin Ireland sun halarci bikin aurensa da matarsa, Bassima, wadda ita ma tana taimaka wa masu wanzar da zaman lafiya da ayyuka wajen fassara.
Sai dai yayin da Ali ke girmama kasancewar sojojin, yana cike da bakin cikin cewar suna can ne don sa ido kuma sun daɗe a can.
"Maganar gaskiya ba mu taɓa tsammanin cewa aikinsu zai kai tsawon shekara 44 ba, " in ji shi.
Ga Bassima kuwa, ta ce yaƙin da ake yi a yanzu ya dawo musu da raɗaɗin na can lokacin rikicin baya, kamar yaƙin Isra'ila da Hezbollah a 2006.
"Ina saka yarona a cikin injin wanki saboda ina fatan cewa hakan zai tseratar da shi," in ji ta.
"Yanzu, mun ci gaba da jin ƙarar waɗannan ababen fashewa kuma ba zan iya jure wa hakan ba.'
Ta yi imanin cewa tashiwa a muhallin da tashin hankali ya dabaibaye shi ya shafi ɗanta, wanda yake da shekara 23 yanzu. Yana firgita idan ya ga jiragen helikwafta na dakarun wanzar da zaman lafiya na MDD na shawagi a sama.
"Ba za mu iya komawa wajen da muke ba," in ji ta. "Muna ɓata rayuwarmu daga wannan rikici zuwa wancan, ba zan iya jure wa ganin wani yaƙi ba."
Komawa ga sansanin, kwamandan Unifil Laftanar Kanar Cathal Keohane ya damu da cewa yawan tashin hankali a yankin yana ƙaruwa.
"Mun ga ƙaruwar hare-hare a can ciki Lebanon, mun ga ana amfani da makamai da dama," in ji shi, yana mai nuna damuwa cewa lamarin na iya ta'azzara.
"Ko da gangan ya taso daga ɓangare guda, ko kuma wasu yanayi ne suka haddasa ɓarkewar yakin, wannan lamari ne mai matukar damuwa a gare mu."
Ya yi fatan cewa tsagaita wuta a Gaza za ta kai ga samun sassaucin zaman ɗar-ɗar a kewayen iyakar Isra'ila da Lebanon, amma ya ce za a iya ɗaukar lokaci kafin ƴan gudun hijira su koma gidajensu, ko da kuwa an kawo karshen faɗa a kan iyaka.