Real Madrid ta yi wa Kroos ban kwana a Santiago Bernabeu

An wallafa

Wadda ta lashe La Liga a bana Real Madrid ta tashi ba ci da Real Betis a karawar karshe da Toni Kroos ya yi ban kwana da Santiago Bernabeu.

Ɗan kwallon tawagar Jamus, wanda zai bar yi wa kasar tamaula bayan Euro 2024, an yi masa tarbar girma, inda ƴan wasa suka kama hannayensu kafin a fara tamaula ya biyo ta tsakaninsu ya shiga fili.

Haka kuma an sauya tsohon ɗan ƙwallon Bayern Munich a minti na 86, wanda aka yi ta masa tafi daga ƴan wasa da kuma ƴan ƙwallo.

Kroos ya lashe kofi 22 a kaka goma da ya yi a Real Madrid.

Tun farko Betis ta sa ran ta ci ƙwallo tun kan hutu, bayan da Johnny Cardoso ya buga ta shiga raga a bugun tazara daga Juan Miranda, amma aka ce Marc Roca ya yi satar gida.

Haka kuma Willian Jose ya kara zura wata a raga bayan da suka yi hutu suka koma zagaye na biyu, itama aka ce da akwai satar gida.

Haka kuma Real Madrid ta barar da damarmaki da yawa, musamman ta hannun Vinicius Junior da Rodrygo a wasan karshe na rufe gasar La Liga ta 2023/24.

Real Madrid ce ta dauki La Liga na bana na 36 jimilla, ita ce kan gaba a yawan ɗaukar kofin a Sifaniya.

Saura wasa daya ya rage a gabn Kroos da zai yi wa RReal Madrid shi ne na Champions League da Borussia Dortmund ranar 1 ga watan Yuni a Wembley.

Real Madrid na fatan lashe kofin zakarun Turai na 15 jimilla, yayin da Dortmund mai kofi ɗaya za ta buga wasan karshe na uku a Champions League.