Gwamnatin Ghana ta hana cin nama tsawon wata ɗaya a wani yanki

Asalin hoton, Getty Images
Hukumomi a yankin Upper East da ke arewacin Ghana sun haramta yanka dabbobi da sayarwa da cin nama tsawon wata ɗaya.
Sun ɗauki matakin ne saboda ɓullar wata mummunar cutar numfashi da ake kira Anthrax mai matuƙar hatsari.
Haramcin ya shafi dabbobi kamar shanu da tumakai da awaki da aladu da jakuna don gudun yaɗuwar cutar.
Mutum ɗaya ya mutu, an kuma gano mutum 13 da suka kamu da cutar.
Jami'an lafiya sun ce sun aika samfurin jini zuwa ɗakin gwaje-gwaje don ƙara gudanar da bincike yayin da kuma suke ci gaba da bin sawun mutanen da suka yi hulɗa da waɗanda ake zargin sun kamu da cutar antiras.
Ana zargin cewa waɗanda suka kamu da cutar sun ci naman shanu ne da ke ɗauke da cutar.
Rahotanni sun ce dabbobi 30 ne suka mutu sanadin antiras.
Ana fargabar cutar za ta iya bazuwa
Hukumomin Ghana sun aika ƙarin riga-kafin dabbobi kyauta zuwa yankin na Upper East a ƙoƙarin ganin an shawo kan cutar.
Ana fargabar cewa cutar ta antiras za ta iya bazuwa zuwa sauran sassan ƙasar ta Ghana.
Antiras dai, cuta ce da ƙwayoyin bakteriya suke yaɗawa kuma tana da saurin yaɗuwa matuƙa a tsakanin dabbobi waɗanda suke iya harba wa ɗan'adam.
Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce antiras cuta ce da ke bazuwa daga dabbobi zuwa jikin ɗan'adam kuma akasari tana shafar shanu da tumaki da awakai ne.
Ƙwayar cutar bakteriyar da dabbobin ke fitarwa, tana samar da wani sinadari mai guba da ke bayyanar da alamomin cuta, kuma tana zuwa da matuƙar hatsarin kisa.
Ɗan'adam na iya ɗaukar cutar daga dabbobin da suka kamu da antiras ko kuma ta hanyar cin naman da ya gurɓata da ƙwayar cutar.












