Ku San Malamanku tare da Malam Usman Nagoda

Bayanan bidiyo, Ku San Malamanku tare da Malam Usman Nagoda
Ku San Malamanku tare da Malam Usman Nagoda
An wallafa

A wannan mako, shirinmu na Ku San Malamanku ya tattauna da malamin addinin Musulunci Malam Usman Nagoda da ke birnin Kano.

An haifi malamin ne a birnin na Kano cikin 1977.

Ya fara karatun allo ne a wurin kakansa, Malam Danjuma Mai Tosaro.

Malamin ya ce daga nan ne ya shiga makarantar firamare ta Magwan, kuma bayan ya kammala ya tafi Sakandire a Kazaure.

Ko da yake, ya koma makarantar Sakandire ta Gwale a birnin Kano inda ya kammala karatu.

Ku kallo bidiyon da ke sama don sauraren cikakken tarihin malamin: