Na taba mafarkin zama limamin Masallacin Annabi (SAW) - Farfesa Ayagi
An haifi Malami Muhammad Sani Musa Ayagi a unguwar Ayagi da ke cikin birnin Kano, a shekarar 1976.
Ya fara karatun Alkur’ani daga gida a hannun mahaifinsa, da kankantar shekaru ya yi sauka.
Ya kuma yi karatun littattafan addini wajen malamai daban-daban a cikin unguwarsu ta Ayagi.
Littattafan sun hada da na fannin Fiqihu da Lugga, da Tajweed, da Nahwu, da Hadisai (Buluqul Mara da RiyadisSalihin) da sauransu.
Da taimakon mahaifiyarsa, ya samu shiga makarantar boko ta Muhammadu Rabi’u da ke unguwar Gwauron Dutse, wadda Arabiyya da boko ake koyarwa, inda ya kammala firamare a shekarar 1987.
A matakin sakandare ya yi makarantar Kofar Ruwa, zuwa aji uku, daga nan ya karasa a makarantar Arabiyya ta SAS.
Ya mallaki shaidar matakin difloma a makarantar Ligal (Legal) da ke Kano. Ya samu damar yin karatun digiri a Jami’atul Islamiyya da ke Madina a kasar Saudiyya.
Sai digiri na biyu da digirin digirgir, a fannin tafsiri da harshen Larabci a Jami’atul Afriqiyya da ke birnin Khartoum na kasar Sudan.
A halin da ake ciki dai Malam Musa Ayagi ya zama farfesa a jami’ar Bayero da ke Kano.
Malamin ya ce babban abin da ya sanya shi farin ciki shi ne lokacin da ya haddace Alkur’ani.
Sai kuma lokacin da ya samu aiki a jami’ar Bayero.
"Babban abin farin cikin da ya same ni da ke faranta min rai shi ne mafarkin da na yi na zama Limamin masallacin Annabi Muhammad (SAW) da ke Madina, inda na ganni ina ta karatun Alkur’ani a cikin masallacin.
"Allah cikin ikonsa sai aka nada ni limamin babban masallacin da ke cikin Jami’ar Bayero."
Babban burin Malam ya ce shi ne ya samu ikon kafa babbar makarantar koyar da Alkur’ani kan ruwayar warshu, yara su taso cikin karatun, a tarbiyantar da su kan tafarkin da Alkur’ani ya tanada.



