Ku San Malamanku tare da Malam Mu'azzam Sulaiman Khalid
Shirin Ku San Malamanku na wannan makon ya karɓi baƙuncin Malam Muazzam Sulaiman Khalid, wanda aka haifa a Unguwar Soron-Ɗinki da ke Jihar Kano.
Malamin ya taso tare da fara karatunsa na allo a cikin garin na Kano a hannun yayan mahaifinsa Malam Datti.
Ya yi karatun Islamiyya a wajen mijin yayarsa mai suna Malam Ibrahim Ci gari. Kazalika, ɗan uwansa ma ya koya musu littafin Kawa'idi.
Ya fara karaunsa na firamare a makarantar Sheikh Nasiru Kabara, shugaban Ɗariƙar Ƙadiriyya a Kano, yayin da ya yi sakandaren koyon Larabci ta SAS.
Malamin ya samu shaidar difiloma daga kwalejin shari'a ta Aminu Kano kafin daga bisani ya samu tallafin karatu a Jami'ar Musulunci ta birnin Madina da ke Saudiyya.
Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, Malam Muazzam na dab da kammala digirinsa na uku.



