Shirin da Zouma ke yi na komawa Shabab Al-Ahli ya bi ruwa

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Shirin da Kurt Zouma ke yi na komawa taka leda a Haɗaɗɗiyar Daulal Larabawa a ƙungiyar Shabab Al-Ahli daga West Ham ya bi ruwa.

An samu matsala a lokacin da aka auna koshin lafiyar mai tsaron bayan ɗan kasar Faransa.

Mai shekara 29 ya je Dubai, domin ƙulla yarjejeniya, sai dai yanzu wakilinsa na neman masa wata mafita.

Zouma yana da sauran ƙunshin ƙwantiragin kaka ɗaya a West Ham, wadda tuni ta ɗauki aron mai tsaron baya, Jean-Clair Todibo daga Nice.

An kuma ƙulla yarjejeniyar cewa za ta iya sayen matashin mai shekara 24 kan £34.22m idan ya taka rawar gani.

Zouma ya buga wasa103 a West Ham tun bayan da ya koma ƙungiyar daga Chelsea kan £29m a 2021.

Ɗan ƙwallon tawagar Faransa, wanda ya lashe Premier League biyu da Champions League a Chelsea, an naɗa shi ƙyaftin ɗin ƙungiyar, bayan da Declan Rice ya koma Arsenal.