Falalar bikin Maulidin manzon Allah

Asalin hoton, Getty Images
Malaman addinin Musulunci sun bayyana falalar da ke cikin yin bikin maulidi.
Malam Haruna Salisu Alfindiki, limamin masallacin Unguwar Alfindiki da ke birnin Kano, ya shaida wa BBC cewa "yana daga cikin ladabi a lokacin maulidi mutum ya yi kyakkaywar niyya da tabbatar da soyayyar annabi Muhammad (SAW)."
Ya kara da cewa bai kamata masu yin maulidi su rika yin ayyukan da suka saba wa shari'a ba.
"Cikin ladabin da masu maulidi ya kama su yi akwai girmama manzon Allah da jin tarihinsa da jin karatuttuka don wata falala da ake samu ita ce mutum yana jin ilimin da bai karanta ba - saboda malamai suna nutsawa su yi bincike su fito da gwala-gwalai na girman manzon Allah da abin da ya shafi nasabarsa da hakurinsa," in ji malamin.



