Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ko Barcelona za ta bai wa Real Madrid tazarar maki biyar ranar Talata?
Barcelona ta ziyarci Osasuna ranar Talata, domin buga wasan mako na 14 a gasar La Liga.
Bayan wasannin mako na 14 za a yi hutu domin Gasar Kofin duniya da Qatar za ta karbi bakunci daga 20 ga watan Nuwamba zuwa 18 ga watan Disambar 2022.
Barcelona za ta yi wasan a matakin mai jan ragamar babbar gasar tamaula ta Sifaniya da tazarar maki biyu tsakaninta da Real Madrid ta biyu.
Real Madrid ta yi rashin nasara da ci 3-2 a gidan Rayo Vallecano a wasan mako na 13 ranar Litinin, karon farko da aka doke ta a bana a gasar.
Barcelona ta dare matakin farko ne, bayan cin Almeria 2-0 a karshen mako a karawar da Gerard Pique ya yi wa kungiyar ban kwana.
Idan Barcelona ta yi nasara a kan Osasuna za ta bai wa Real Madrid tazarar maki biyar tsakani a teburi daga nan a yi hutun buga Gasar La Liga.
To sai dai Osasuna na taka rawar gani a kakar nan, wadda take ta biyar a kan teburin babbar gasar tamaula ta Sifaniya.
A wasannin baya da kungiyoyin suka kara Barcelona ba ta da tabbacin samun maki uku a karawar da take ziyartar El Sadar.
Tuni Xavi ya bayyana 'yan wasa 22 da ya je da su Osasuna ciki har da Pigue.
Watakila Pique ya buga fafatawar bayan da mai tsaron baya Ronald Araujo da Sergi Roberto da Jules Kounde ke jinya.
Barcelona ta kira matasa biyu daga karamar kungiyar Marc Casadó da Chadi Riad, domin maye gurbin Frank Kessi da Memphis Depay, wadanda ke jinya.