Tsohon dan kwallon Ingila Jagielka ya sanar da yin ritaya

An wallafa

Tsohon dan wasan Ingila, Phil Jagielka ya sanar da yin ritaya daga taka leda, mai shekara 41.

Jagielka ya rataye takalmansa, bayan buga wasa sama da 800 a kaka 23 da ya yi yana sana'ar taka leda.

Jagielka ya fara wasa a Sheffield United, wadda ya yi kaka takwas daga nan ya koma Everton a 2007.

A goodison Park ya yi shekara 12, har ya zama kyaftin din kungiyar a 2013, amma sai ya sake komawa Sheffield, bayan da yarjejeniyarsa ya kare a Everton a 2019.

Daga nan ya yi kaka biyu a Sheffield, bayan da kungiyar ta koma buga Premier League, sannan ya yi wata shida a Derby, daga nan ya yi ritaya aStoke City.

Ya buga wa Ingila wasa 40 tsakanin 2008 zuwa 2016 ya kuma wakilci kasar a Euro 2012 da gasar cin kofin duniya a 2014 da aka yi a Brazil.