Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Bukukuwan Maulidi da tsinkar inabi cikin hutunan Afirka
Zaɓaɓɓun ƙayatattun hotunan Afirka da na 'yan nahiyar a wasu sassan duniya
A Talatar da ta gabata ne aka yi bikin tsinkar inabi a Tunisia
Musulmi a sassan duniya sun yi bikin Maulidin Annabi Muhammad (S.A.W) a Masar, an fara bikin ne a ranar Juma'a.
Wani yaro yana tura kekensa cikin ruwa a birnin Maiduguri, yayin ambaliyar ruwa.
A Senegal, matasa sun taru dandalin Seydina Limamou Laye, a Dakar babban birnin ƙasar.
A Tunisian ma an yi bikin maulidin a kan titunan ƙasar a ranar Lahadi.
An binne ƴar wasan tseren Uganda, Rebecca Cheptegei, wadda saurayinta y kashe.
Sojojin Uganda sun yi faretin girmamawa da harba bindiga a sama domin karrama mariganya Rebecca.
Mutane na hutawa a wata gaɓar teku da ke Suez Canal a ƙasar Masar.
Masu aikin ceto na ƙoƙarin zaƙulo mutanen da rushewar gini ya ritsa da su a Freetown babban birnin Saliyo, a ranar Litinin.