Zanga-zangar Larabawan Isra'ila game da garambawul a ɓangaren shari’a

An wallafa

A gangamin baya-bayan nan na tunawa da zagayowar ranar Larabawa ‘yan kasar Isra’ila da kuma Palasdinawa da ake kira Land Day, Jameel Saed ya yi tur da zanga-zanga a fadin kasar kan shirin yi wa bangaren shari’a garanbawul mai cike da cece-kuce da ya mamaye kasar ta Isra’ila tun a farkon wannan shekarar.

"Ban taba shiga cikin ko wace irin zanga-zanga ba kuma ba zan yi ba. Ba na jin cewa Palasdinawa sun shiga,’’ a cewa dalibi daga birnin Nazareth na Larabawa a arewacin kasar Isra’ila.

"Zanga-zangar Isra’ila na yin kira da dawo da tsarin yadda yake a baya – don neman a dawo tarakin dimokaradiyya’. Amma ba ma jin cewa wani abu ne ba zalunci ko nuna wariyar launin fata ba.

"Wannan ba abinda muke so ba ne."

Jameel daya daga cikin Larabawan Isra’ila miliyan biyu. Larabawan Isra’ila Palasdinawa ne da kaka da kakanninsu da suka zauna a kasar da ta zama Isra’ila a shekarar 1948 ne. Sun kuma kunshi kashi 20 bisa dari na yawan a’lummar Yahudawa.

A yayin da a hukumance ‘yan kasar Isra’ila ne, da dama – kididdiga da kuri’u sun karkasu – na ayyana kai a matsayin Palasdinawa.

Dubban daruruwan masu zanga-zanga ne kan bazu a kan titinan isra’ila a ko wane mako.

Suna gudanar da zanga-zanga a kan gwamnatin kasar kan garanbawul da zai kara mata karfin iko a kan nada-naden babbar kotu da yanke shawarwari.

A yayin da ake cikin hargitsi a faruruwa da biranen Isra’ila, gwamnatin hadaka ta Firaminsta Benjamin Netanyahu yanzu ta dakara ta garanbawul din na akalla sai majalisar dokokin Isra’ila da dawo daga hutu a ranar 30 ga watan Aprilu.

Jameel ya yi amanna cewa gangamin na ranar ta Land Day – taron gangamin shekara-shekara na tunawa da kisan da sojojin Isra’ila a shekarar 1976 suka yi wa Palasdinawa shida kan matakin da suka dauka game da kwace musu matsugunan da Isra’ila ta yi – ya fi muhimmanci ga ‘yancin Palasdinawa a kan shiga cikin gagarumar zanga-zangar.

Game da gangamin a garin Sakhin na Larabawan Isra’ila, inda aka aikata wasu daga cikin kashe-kashen, ya dasa ayar tambaya kan nuna banbanci da jami’an tsaron Isra’ila ke nunawa tsakanin zanga-zangar Palasdinawa da ta Yahudawa.

"Muddin muka yi daya bisa uku abinda Yahudawa ke yi da yanzu an kashe mu,’’ ya ce.

Nuna bambanci da wariya

A cikin duka zanga-zangar da ake gudanar, shiga cikin da Larabawan Isra’ila suke yi kadan ce kana da farkon fari a yankunan Larabawan Isra’ilar ne da ke arewaci.

Wasu na farin cikin ganin kace-nace kan bangaren shari’a ya taka muhimmiyar rawa, ko kuma na tunanin sakamakon tsarin kasar wanda da dama ke ganin a ko da yaushe ana ware a’lummarsu daga samun cikakken ‘yancin demokaradiyya.

Da dama na cewa hukunce-hukuncen baya na Kotun Koli da suna nuna wariya a kan Paladinawa, a Isra’ila da kuma yankunan da aka mamaye, ba su bayar da wani karsashin kare wa ba. Alal misali, dakatar da dokar kasar da ta tanadi cewa a Isra’ila ‘yancin nuna jajircewa na Yahudawa ne kawai.

A baya-bayan nan, kotu ta amince da fitar da Palasdinawa 1,000 daga yankunansu a yankin Gabar Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye saboda sojojin Isra’ila su yi amfani da su wajen yin atisaye. Kwararru a fannin kare hakkin biladama na Majalisar Dinkin Duniya sun yi gargadin cewa matakin – ka iya haifar da aikata laifukan yaki.

Bayan gudanar da jeren zabukan da bas u kammala ba a Isra’ila, zaben watan Nuwaba ya sa Mista Netanyahu sake komawa kan karagar mulki.

Da mulkin hadakar gwamnatin jam’iyun masu kishin kasa da na addini, Palasdinawa da dama da yankin Gabar Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye na ganin alamun barazanar a fannin dokoki da al’adu da siyasar ta.

Biyu daga cikin fitattun ministoci a gamayyar – Minsitan Kudi Bezalel Smotrich da Ministan Harkokin Tsaron Kasa Itamar Ben-Gvir – su kan su ‘yan kama-wuri-zauna ne a Gabar Yammacin Kogin Jordan.

A watan da ya gabata, Mista Smotrich ya takalo gagarumin martani a loakcin da ya ce babu wani abu mai kama da wani abu wai al’ummar Palasdinawa.

Masu sharhi a kafar yada labaran Isra’ila sun yi has ashen cewa gwamnatin hadakar za ta yi kokarin soke dokokin da ke taka mata birki wajen hadewa da wasu ko duka yankin Gabar Yammacin Kogin Jordan din. Muddin wannan mataki ya tabbata, akwai yiwuwar korar ko hadewa da Palasdinawan.

'Ba mu kadai ba ne'

Zanga-zangar ta biya bukatun kiraye-kiraye daga Yahudawa ‘yan kasar Isra’ila kan ‘yancin Palasdinawa, da mamata da kuma zaman lafiya ya kasance bangare ta zaman tattaunawa.

Amma kuma, duk da halin da ake ciki, wasu Larabawan Isra’ila na kara yin mats ikan a kaa gudanar da kara shiga cikin gagarumar zanga-zangar Isra’ila.

A gangamin na ranar Land Da, Aida Touma-Suleiman, wani Balarabe dan majalisa ya ce: ‘’ Wau za su shiga, amma ba kamar yadda ake tsammani da wadanda wadannan garanbawul za su yi wa nakasu ba.

"Wadanda suka siyasantar da komai kamar mu, muna kokarin yin matsin lamba don aji muryoyinmu, ko ta hanyar zaman tattaunawa da wadanda ke jagorantar zanga-zangar ko suke cikin zanga-zangar a karkashin kungiyar yaki da cin hanci da rashawa.’’

Wannan kungiya ana kara ganin ta a cikin manya zanga-zanga kana na biranen This bloc Tel Aviv da Kudus, na daga tutocin Palasdinu tare da rera take a cikin harsunan Hebrew da kuma Larabci.Duk da cewa har yanzu kadan ne idan aka kwatanta da yawan adadon masu zanga-zangar.

Wasu Larabawan Isra’ila na yi wa zanga-zangar kallon wata dama da kara karfin neman bukatar daidato.

"Muna cewa ne dimokradiyyar gaskiya ba za ta taba wanzuwa ba muddin akwai mamayar yankunan wasu mutane – Palasdinawa – kana cewa dimokaradiyyar gaskiya ba za ta taba zama main una banbanci a kan Palasdinawa ‘yan kasar Isra’ila ba,’’ a cewar Yousef Jabareen, wani Balarabe, dan majalisar dokokin kana malami a fannin karatun lauya.

"Akwai bukatar bullo da wasu tsare-tsare bunkasa dimokradiyya.’’

Ya kunshi aiki tare da Yahudawan Isra’ila.

A ranar Asabar din farko ta zanga-zanga a birnin Tel Aviv lokacin hutun majalisar dokoki, Alon-Lee Green na cikin wasa masu zanga-zangar da ke sanye da rigunan shat masu launin algashi da ke tattare wuri guda.

Mr Green mataimakin daraktan kungiyar Standing Together mai hada kawunan Palasdinawa da Yahudawa don cimma burin zaman lafiya da daidaito ne.

Ya bayyana cewa neman a ji muryoyinsu ya kasance da matukar wahala, amma an kaar samu karfin guiwa.

"Akwai gagarumar muhawara a cikin zanga-zangar (kan hadawa da yin kiraye-kiraye kan ‘yancin Palasdinawa),’’ ya ce.

Ya ce jama’a da dama ba sa so a kawo batutuwan kama-wuri-zaunan ko yi wa al’umma adalci a zanga-zangar.

A baya a kwai hare-hare da dama, har da da munanan hare-hare a kan mutanen da ke rike da tutocin Palasdinu a cikin wadancan zanga-zangar,’’ ya ce.

Ibrahim Abu Ahmad, wanda ke aiki ga kungiya mai zaman kan ta, daya daga cikin Larabawan Isra’ila ne da suka yi magana a lokacin gangamin Isra’ila.

Ya goyi bayan gine-gine a Isra’ila da karfafa ayyukan siyasa da zamantakewar Palasdinawa.

"Muna da wani aminai a cikin wannan al’umma ta Yuhdawa, ba mu kadai ba ne, akwai mutanen da suka yi amanna da wannan sauyi,’’Mr Abu Ahmad ya ce. "Ya kamata mu dauke shi a matsayin wata dama ta saka su a gefen mu. Kuma kada mu cire kan mu daga komai.’’

"Daga nan bayan shawo kan tashin hankalin za mu iya cewa: ‘Mun tsaya muku. Yanzu lokaci ya yi da za mu tattauna a kan matsalolinmu.’’

Mr Abu Ahmad ya kara da cewa ‘’ bai kamata mu jira wani izini ba’’ wajen mika kokenmu da ra’ayinmu.

"Ya kamata mu yunkura,’’ ya ce.