Kano Pillars ta naɗa Abdu Maikaba sabon kocinta

Asalin hoton, Twitter/Kano Pillers
Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta nada Abdullahi Maikaba a matsayin sabon kocinta.
Maikaba ya rattaba hannu kan kwangilar shekara biyu da kungiyar da ake kira ''Sai Masu gida'' daga kakar 2023/2024 zuwa 2024/2025.
Kociyan zai yi aiki tare da Abubakar Abubakar da ake kira Senior da Ahmad Garba Yaro Yaro da Gambo Muhammad da kuma Auwalu Abbas a matsayin mai horar da masu tsaron gida.
Da yake kaddamar da kocin a ofishinsa, mataimakin gwamnan jihar Kano, Kwamared Aminu AbdulSalam Gwarzo, ya bukace shi da ya zage damtse domin farfado da martabar kungiyar.
Mataimakin gwamnan, ya taya shi murna tare da bayyana nadin nasa a matsayin wanda ya dace ganin irin dumbin kwarewarsa a harkar koyar da kwallon kafa a kungiyoyin daban-daban a Najeriya.
Mataimakin Gwamnan ya yi alkawarin ci gaba da bai wa kungiyar goyon baya domin ganin an cimma burin da aka sanya a gaba, sannan kuma ya bayar da tabbacin cewa nan ba da jimawa ba gwamnatin Kano za ta kara kaimi wajen gyaran filin wasa na Sani Abacha da ke kofar mata Kano.
Ya yaba wa shugabannin kungiyar da ‘yan wasan kungiyar bisa kwazon da suka nuna wanda ya sa kungiyar ta koma gasar Premier.
Da yake mayar da martani, Abdullahi Maikaba ya gode wa mahukuntan kungiyar da suka amince da shi sannan ya yi alkawarin tabbatar da amincewar da aka yi masa.
A bara ne Pillars ta fadi daga gasar Firimiya ta kasar, wadda ta koma buga gasa mai daraja ta biyu, wadda za ta buga babbar gasar tamaula ta bana a Najeriya.











