Rangers ta kori kociya Giovanni van Bronckhorst

An wallafa

Rangers ta raba gari da kociyanta Giovanni van Bronckhorst, bayan shekara daya yana horar da ita.

Dan kasar Netherlands ya karbi aikin cikin watan Nuwambar 2021, wanda ya ja ragamar kungiyar ta buga wasan karshe a Europa League da lashe Scottish Cup.

Sai dai kungiyar ta kasa taka rawar gani a Champions League da rashin kwazo mafi muni a tarihin kungiyar a karawar Zakarun Turai.

Ranar 12 ga watan Nuwamba Rangers ta tashi 1-1 da St Mirren, hakan ya sa ta barar da maki a karawa uku daga biyar, bayan rashin nasara a hannun St Johnstone da canjaras a gida da Livingston.

Haka kuma doke ta da kwallaye da yawa da Celtic ta yi da kuma shan kashi a Champions League a hannun Ajax da Liverpool da Napoli, sune suka kara jefa kocin cikin matsi.

Rangers ta yi nasara a kan Union Saint-Gilloise da kuma PSV Eindhoven a wasannin neman gurbin shiga Champions League, ta yi rashin nasara a fafatawa tara a wasa 27 da ta yi da cin 14.

Kungiyar za ta fafata da Aberdeen a wasan daf da karshe a League Cup, sannan ta fara karawar kare kofinta a Janairu.