Arteta na sa ran za a yi wa Rice tarbar girma a West Ham

Decline Rice

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Kociyan Arsenal, Mikel Arteta ya ce yana fatan West Ham za ta yi wa Declan Rice tarbar girma a wasan kofin Carabao da za su fafata ranar Laraba.

Mai shekara 24 dan kwallon tawagar Ingila ya koma Gunners daga West Ham kan fam miliyan 105 kafin fara kakar bana.

Ya yi wa West Ham kyaftin lokacin da kungiyar ta lashe Europa League a cikin watan Yuni, kofin farko da suka lashe tun bayan 1965.

''Wannan shi ne karonsa na farko da zai fuskanci kungiyarsa, wani yanayi mai kayatarwa a wajensa.'' in ji Arteta.

Rice ya koma West Ham yana dan shekara 14 daga nan ya buga mata wasa 245 jimilla, daga nan ya koma Arsenal.

Gunners tana ta biyu a teburin Premier League kuma Arteta ya sauya 'yan wasa takwas daga wadanda suka doke Brentford 1-0 a gasar - kociyan ya nanata cewar Caraboa Cup yana da mahimmaci a wajensa.

Gabriel Jesus ba zai buga wasan ba, sakamakon jinya tare da Thomas Partey, bayan da ake sa ran kyaftin, Martin Odegaard zai huta, wanda ke murmurwa daga jinya.

A bangaren West Ham kuwa 'yan wasanta Vladimir Coufal da mai tsaron raga, Lukasz Fabianski sun murmure, wadanda ba su buga wa kungiyar Europa League ranar Alhamis da Olympiakos.

Sai dai Coufal an fara wasa da shi lokacin da Everton ta ci West Ham 1-0 a ranar Asabar a gasar Firimiyar Ingila.

West Ham tana mataki na tara a Premier League, wadda ba ta ci wasa hudu ba a baya-bayan nan, har da ukun da aka doke ta a jere a dukkan karawa.

Decline Rice

Asalin hoton, PA Media