Ƙayatattun hotuna daga sassan nahiyar Afirka

Ranar Litinin aka gudanar da wasan tsaren doki a garin Luxor, na kasar Masar.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ranar Litinin aka gudanar da wasan tsaren doki a birnin Luxor, na kasar Masar. Inda mutane da dama daga ciki da wajen birnin suka hallara domin kallon wasan.
An wallafa
Wannan mutumin na daga cikin mutanen da suka shiga wasan tseren.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wannan mutumin na daga cikin mutanen da suka shiga wasan tseren.
Nan kuma wasu mata ne ke cefane a kasuwar birnin Tripoli na kasar Libya, gabanin bikin Maulidin Annabi Muhammadu S.A.W

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Nan kuma wasu mata ne ke cefane a kasuwar birnin Tripoli na kasar Libya, a shirye-shiryen bikin Maulidin Annabi Muhammadu S.A.W
Tauraruwar fina-finan Uganda da Birtaniya Sheila Atim,

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Tauraruwar fina-finan Uganda da Birtaniya Sheila Atim, lokacin da aka dauki hotonta a yayin bikin nuna wani fim mai suna 'The Woman King' a birnin Landan. Fim din ya kunshi wasu abubuwan ban mamaki da suka faru a karni na 18, da na 19 a daular Dahomey, wanda a yanzu ke cikin kasar Benin.
Wacce ta taka rawa a matsayin wata jaruma da ke kokarin kare daularta a cikin fim din.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A dai wannan bikin ne aka dauki hoton wannan jarumar fina-finai ta Afirka ta kudu Thuso Mbedu - Wacce ta taka rawa a matsayin wata jaruma da ke kokarin kare daularta a cikin fim din.
Bikin ya samo asali tun shekara 800 da suka gabatar

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Nan kuma a garin Tangier-Tetouan ne na kasar Morocco ranar Asabar, inda wannan matar ke cikin nishadi a wani bikin tsaren doki mai tsohon tarihi da aka gudanar a kasar ranar Asabar. Bikin ya samo asali tun shekara 800 da suka gabatar
Idan muka leka Birtaniya kuma nan wasu matasa biyu lokacin da suke halartar bikin baje kolin ayyukan zane-zanen wani dan Najeriya.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Idan muka leka birnin Landan kuma nan wasu matasa biyu 'yan Najeriya lokacin da suke halartar bikin baje kolin ayyukan zane-zanen.
An baje-kolin ayyukan zane-zane da dama a gidan ajiye kayan tarihi na Serpentine South Gallery da ke birnin Landan ranar Alhamis.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An baje-kolin ayyukan zane-zane da dama a gidan ajiye kayan tarihi na Serpentine South Gallery da ke birnin Landan ranar Alhamis.Inda wata mai zane-zane daga kasar Sudan mai suna Kamala Ibrahim Ishag, ta hallara domin gabatar da ayyukanta.
Mista Obi na daya daga cikin manyan 'yan takarar shugaban kasar Najeriya a zaben 2023.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wannan kuma wani magoyin bayan dan takarar shugaban Najeriya karkashin jam'iyyar Labour party Peter Obi lokacin da dan takarar ha halarci gangamin yakin neman zaben da ya tara dubban mutane. Mista Obi na daya daga cikin manyan 'yan takarar shugaban kasar Najeriya a zaben 2023.
Nan kuma wasu matasa ne ke wasa da babur mai kafa uku

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Nan kuma wasu matasa ne ke wasa da babur mai kafa uku, a lokacin gangamin yakin neman zaben.
An kiyasta cewa mutum 800,000 ne suka mutu akasarinsu 'yan kabilar Tutsi a cikin kwana 100 da aka shafe ana gwabza fadan.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wata 'yar gidan sarautar Birtaniya a birnin Kigali ke duba hotunan wasu daga cikin mutanen da suka mutu a lokacin kisan kiyashin Rwanda da aka gudanar a shekarar 1994.An kiyasta cewa mutum 800,000 ne suka mutu akasarinsu 'yan kabilar Tutsi a cikin kwana 100 da aka shafe ana gwabza fadan.
Reuben Kiprop Keiro dan asalin kasar Kenya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Reuben Kiprop Keiro dan asalin kasar Kenya kenan lokacin da yake murnar lashe gasar tseren gudu karo 99 da ka gudanar a kasar Slovakia ranar Lahadi.
Abin da kuma ke shafar miliyoyin mutane a yankin gabashin Afirka

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Nan kuma a gandun namun dajin LKenya ne lokacin da aka dauki hoton wannan rakumin dawa a yayin da mummunan farin da ake fuskanta a yankin ke yin barazana ga gandun dajin,.Abin da kuma ke shafar miliyoyin mutane a yankin gabashin Afirka, a yayin da dabbobi da dama ke mutuwa sakamakon matsanancin halin da suke ciki.
Idan muka koma arewacin Afirka kuma, nan masu gadin kan iyakar kasar Tunisiya ne suka kubutar da wasu 'yan cirani

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Idan muka koma arewacin Afirka kuma, nan jami'an da ke kula da kan iyakar Tunisiya ne suka kubutar da wasu 'yan cirani a lokacin da ake kokarin tsallakar da su ta kwale-kwale domin safararsu zuwa kasashen Turai.
A birnin Kampala na kasar Uganda, jami'an 'yan sanda suka kama wani dan gwagwarmaya

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, A birnin Kampala na kasar Uganda, jami'an 'yan sanda suka kama wani dan gwagwarmaya lokacin da yake jagorantar wata zanga-zangar nuna goyon baya ga kudurin majalisar tarayyar Turai na dakatar da aikin shimfida bututun iskar gas da kasashen gabashin Afirka ke kokarin yi, wanda suke gani a matsayin wani abu da zai kawo illa ga muhalli.
okacin bikin kaddamar da littafin tarihin rayuwar hamshakin dan kasuwar kasar Patrice Motsepe.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sarauniyar kyau ta Afirka ta kudu, Ndavi Nokeri (tsakiya), da marubuciya Nhlanhla Shezi , da kuma 'yar jarida Janet Smith, a lokacin bikin kaddamar da littafin tarihin rayuwar hamshakin dan kasuwar kasar Patrice Motsepe.