Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Chelsea ta kafa tarihin cin kwallo takwas a Conference
Chelsea ta ci kwallaye mafi yawa a tarihin gasar Conference bayan yi wa kungiyar FC Noah ta Aremnia ruwan kwallaye.
Blues na buga wata irin kwallo kamar ba su ba tun daga wasan da suka buga na ƙarshe a Premier, sun ci 6-0 gabanin hutun rabin lokaci suka ƙara biyu bayan an dawo.
Tun fara ne da cin kwallo a kwanar da Enzo Fernandez ya kwaso Tosin Adarabioyo ya sa mata kai.
Da sa kwallon Noah suka yi kuskuren da Marc Guiu ya ɗauke ya zura kwallo ta biyu.
Axel Disasi ya ƙara ta uku a wata kwanar da Enzo ya ƙara kwasowa, sai Enzo ɗin dai ya sake bai wa Joao Felix kwallo ta hudu da ya ɗaga wa golan ita ta shiga raga.
Mykhailo Mudryk ya ci kwallo mafi kyau a wasan ne wadda ita ce ta biyar inda ya buga ta ƙarshen raga, gabanin Felix ya ƙara ta biyu da ya ci a wasan ta shida ga Chelsea wadda ta daki jikin wani ta shiga.
Christopher Nkunku da ya buga kwallo ta daki turke ba ta shiga ba, ya ci ta bakwai ga Chelsea.
Kuma ɗan wasan na Faransa ya ci bugun fenareti kwallo tatakwas kenan a wasan.
A tarihin gasar waɗannan ne kwallayen da aka ci mafi yawa tun bayan fara ta.