Yadda ziyarar shugaban Ukraine ta kasance a Amurka

Bayanan bidiyo, Ga yadda ziyarar shugaban Ukraine ta kasance a Amurka cikin minti daya da rabi
Yadda ziyarar shugaban Ukraine ta kasance a Amurka
An wallafa

Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya yi wani jawabi da ken una jajircewa ga majalisar dokokin Amurka a ziyararsa ta farko da ya yi zuwa wata ƙasa tun bayan kutsen Rasha ƙasarsa.

Ya ce Ukraine ba ta durƙushe ba kuma ba ta yi ƙasa a gwiwa ba sannan ba za ta taɓa miƙa wuya ba.

Shugaba Joe Biden ne ya karɓi baƙuncin Mr Zelensky a Fadar White House sannan ya samu karɓa ta karramawa daga ƴan majalisar dokokin.

Ga dai yadda ziyarar ta kasance a cikin wannan bidiyon mai tsawo minti daya da rabi.