Arsenal za ta buga Champions League karon farko bayan 2016/17

Asalin hoton, Champions League
Arsenal za ta karɓi baƙuncin PSV Eindhoven a Emirates ranar Laraba a wasan farko a cikin rukuni a Champions League.
Karon farko da Gunners wadda ta buga Europa League za ta koma karawa a babbar gasar tamaula ta Turai tun bayan 2016/17.
Wannan shi ne wasa na tara da za su kara a tsakaninsu, inda Arsenal ta ci wasa uku da canjaras uku, PSV ta yi nasara a biyu.
Sun kuma fafata ne sau shida a Champions League da kuma wasa biyun da suka kara a Europa League a bara.
Sun fara wasa a Champions League ranar Laraba 25 ga watan Satumbar 2002 a Eindhoven, inda Gunners ta ci 4-0.
PSV tana da Champions League ɗaya da ta ɗauka a shekarar 1987/1988, yayin da har yanzu Gunners ke fata.
Ɗaya wasan rukuni na biyun za a yi ne tsakanin Sevilla da RC Lens.
Jerin wasa tsakanin Arsenal da PSV Eindhoven:
Kakar 2022/2023 Europa League
- PSV Eindhoven 2 - 0 Arsenal
- Arsenal 1 - 0 PSV Eindhoven
Kakar 2006/2007 Champions League
- Arsenal 1 - 1 PSV Eindhoven
- PSV Eindhoven 1 - 0 Arsenal
Kakar 2004/2005 Champions League
- PSV Eindhoven 1 - 1 Arsenal
- Arsenal 1 - 0 PSV Eindhoven
Kakar 2002/2003 Champions League
- Arsenal 0 - 0 PSV Eindhoven
- PSV Eindhoven 0 - 4 Arsenal











