Liverpool ta fara tattaunawa kan makomar Salah, Chelsea za ta mika Chilwell ga Turkiyya

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Liverpool na shirin bude hanyar tattaunawa kan dan wasan gaba na Masar Mohamed Salah, mai shekara 32, bayan ya sanar da cewa wannan ce kakar wasan shi ta karshe a kulub din, bayan nasarar da suka yi kan kungiyar Manchester United. (Football Insider)

Manajan Pumas UNAM, Gustavo Lema ya ce kungiyar Liverpool ta so daukar dan wasan da ke taka musu leda kuma na Mexico Cesar Huerta, mai shekara 23. (TUDN - in Spanish)

Chelsea ta shirya domin bada dan wasan baya na Ingila Ben Chilwell, mai shekara 27, aro ga kulub din Turkiyya, duk da cewa har yanzu ba bu wanda ya taya dan wasan.(Telegraph - subscription required)

Kungiyar Chelsea da AEK ta Athens na tattaunawa kan dan wasan gaba na Ivory Coast David Datro Fofana mai shekara 21, amma a matsayin bashi. (Mail)

Tottenham ta kammala tattaunawa kan sayan dan wasan tsakiya na Amirka Johnny Cardoso, mai shekara 22 daga Real Betis, kan farashi fam miliyan 21. (Telegraph - subscription required)

Galatasaray na tattaunawa da Manchester United, kan daukar aron dan wasan tsakiya na Barzil Casemiro, mai shekara 32. (Ali Naci Kucuk - in Turkish)

Tsohon dan wasan tsakiya na Liverpool, Naby Keita, 29, na tattaunawa da Basaksehir na Santambul, kan yiwuwar komawa kulub din daga Werder Bremen bayan yarjejeniyar Guinea da ba su cimma matsaya kan komawa Sunderland ba. (Guardian)

An yi wa tsohon dan wasan Manchester United Anthony Martial, mai shekara 28, ta yin kwantiragi da kulub din AEK Athens, kuma zai iya kasancewa dan wasan da aka fi biya albashi mafi tsoka a kulub din.(Sport24 via Sun)

Manchester United na sa ido akan dan wasan baya na Colombia mai taka leda a Juventus Juan Cabal mai shekara 23. (Tutto Juve - in Italian)