Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An aike sakon barazanar kisa ga Potter da iyalansa
Kociyan Chelsea, Graham Potter ya ce ya kadu tare da iyalansa, bayan samun sakon barazanar kisa, sakamakon da kungiyar ba ta kokari a karkashinsa.
Kungiyar Stamford Bridge ta ci wasa biyu daga 14 da ta buga baya a dukkan fafatawa, wadda a makon jiya Southampton ta doke ta a Premier League.
Chelsea ta sanar cewar tana goyon bayan Potter da iyalansa dari bisa dari tana tare da shi.
''Na karbi sakon wasika ta internet, wanda ke dauke da barazanar kisa'' in ji Potter.
''Ba sakone mai mai dauke da kalaman farin ciki da za ka karanta ba.''
Tsohon kociyan Brighton ya ce sakon da ya shafe shi, an kuma hada barazanar kisan har da na iyalansa.
An nada Potter kociyan Chelsea cikin watan Satumba, bayan da ta kori Thomas Tuchel - wasa tara Chelsea ta yi nasara daga 25 baya.
Chelsea tana ta 10 a teburi da tazarar maki 11 tsakaninta da gurbin 'yan Champions League da ke fatan buga wasannin badi.
Ranar Lahadi Chelsea za ta buga wasan hamayya a gidan Tottenham a gasar Premier League mako na 25.
Kungiyoyin biyu sun tashi 2-2 a wasan farko a bana karkashin Thomas Tuchel a Stamford Bridge.