Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda ɗaliban Najeriya ke maular abinci a Birtaniya
- Marubuci, Joanna Morris
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, North East da Cumbria
- Marubuci, Louise Hobson
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Tees
- Aiko rahoto daga, Stockton
- An wallafa
Ɗalibai ƴan asalin Najeriya waɗanda ke fama da matsalar kuɗi su ne suka fi yawa a cikin masu ziyartar wata cibiya da ake bayar da taimakon abinci, kamar yadda shugabar cibiyar ta sanar.
Matsalar tattalin arziƙi ta jefa ɗaliban Najeriya da dama masu karatu a ƙasashen waje cikin halin tsanani, inda suke fafutukar neman abin da za su biya kuɗin makaranta.
Hakan ne ya sa aka dakatar da wasu ɗaliban daga jami'ar Teesside University tare da umurtar su su koma gida.
Shugabar wata cibiyar bayar da tallafin abinci da ake kira Thornaby's Sprouts Community Food Charity (SCFC), Debbie Fixter, ta ce kashi 75 cikin ɗari na masu zuwa neman taimko a cibiyar, ɗalibai ne waɗanda lamarin ya shafa.
Jami'ar ta ce tana tallafa wa ɗaliban ƙasashen waje, kuma dukkanin ɗalibai na ƙasashen waje wajibi ne gare su su gabatar da shaidar cewa suna da isassun kuɗi lokacin da suke neman takardar shiga ƙasar, wato 'visa'.
Cibiyar ta SCFC takan shirya taruka kuma takan sayar da abinci a farashi mai rahusa sosai ko kuma ta bayar kyauta, har ma da kayan sawa da na amfanin gida.
Cibiyar ta bayyana cewa a cikin watannin baya-bayan nan mafi yawan masu zuwa neman taimako ɗaliban Najeriya ne masu karatun digiri na biyu daga jami'ar Teesside University.
Najeriya na fama da matsalar tattalin arziƙi, inda darajar naira ta faɗi da kimanin kashi 200 cikin ɗari idan aka kwatanta da dalar Amurka a cikin shekara ɗaya.
Hakan ya sanya tanadin kuɗi da ɗaliban Najeriya masu karatu a Birtaniya suka yi sun yi ƙasa sosai, lamarin da ya mayar da su suka koma ƴan Allah ba ku mu samu.
Sai dai mai magana da yawun jami'ar ya tabbatar da cewa jami'ar ta Teesside University na ci gaba da ɗaukar ɗalibai daga Najeriya.
'Sun zama wani ɓangare na al'ummarmu'
Shugabar cibiyar bayar da taimako ta SCFC, Ms Fixter ta ce akwai ƙarin ɗaliban Najeriya da je Birtaniya domin karatu, waɗanda ke garzayawa wurin cibiyoyin bayar da taimako domin neman tallafi.
"Suna shan wahala sosai, suna buƙatar taimako, muna ɗaukar su a matsayin wani ɓangare na al'ummarmu," in ji ta.
Wani ɗalibin da ya je neman taimako, Boluwatife Elusakin, ya ce dole sai da ya ƙure kansa a ƙoƙarin yadda zai rufa wa kansa asiri a Birtaniya.
Matsalar tattalin arziƙin da Najeriya ke fuskanta na nufin cewa zai kashe nunkin kuɗin da ya ware na zama a Birtaniya.
Ya ce "Abubuwa sun sauya".
"Dole sai na tsuke bakin aljihu saboda matsalar kuɗi, matsalar ta dagula min lissafin da na yi baki ɗaya.
Abin na baƙanta min rai, amma ina fatan zan iya jure wannan shekara ɗaya da ta rage, daga nan komai zai warware."
Wani ɗalibin wanda bai so a ambaci sunansa ba, ya ce sauya salon biyan kuɗin makaranta da hukumomin jami'ar suka yi - daga biya sau bakwai zuwa sau uku - ya ƙara ta'azzara al'amarin.
Ya kuma ce shirin da ɗalibai suka yi na yin aiki domin cike giɓin kuɗin da zai ishe su rayuwa ya samu tangarɗa sanadiyyar yawan sa'o'in aiki da aka ƙayyade musu.
"Lokacin da na cika takardar neman yin karatu ana sauya fan ɗaya na Birtaniya kan naira 600, amma ya zuwa lokacin da na iso fan ɗaya ya kai naira 1,400," in ji shi.
"A lokacin da muka cike takardar neman yin karatu muna da kuɗin da za su kai mu tsawon wata tara.
"Amma kuɗin ba za su isa ba, babu aiki ga shi kuma kuɗin na ta ƙarewa, mafi yawan mu sun shiga tsanani.
"A duk lokacin da ba ka da kuɗi sai ka shiga mummunan hali, wasu ma sun fara shiga matsalar damuwa.
"Wasu sun yi da-na-sanin zuwa."
'Cibiyar ta cika maƙil'
Ms Fixter ta ce yanzu haka "cibiyarta ta cika maƙil" saboda halin da ake ciki, kuma ta buƙaci jami'ar ita ma jami'ar Teesside ta tallafa.
Ta ce ya zuwa yanzu jami'ar na tallafawa ne kawai ta hanyar bayi wa ɗalibai sabbin zuwa kyautar kati mai ƙunshe da fan 500 wanda za su iya yin sayayya a kantin Sainsbury, sai dai ta ce wannan tamkar "ɗigon ruwa ne a cikin teku" idan aka yi la'akari da irin tuɗaɗar da ɗalibai ke yi zuwa cibiyar.
Jami'ar ta ce ta yi aiki tare da ƙungiyoyin yankin domin tallafa wa ɗalibai ta yadda za a sauƙaƙa wa ƙungiyoyin.
Mai magana da yawun jami'ar ya ce "Ɗalibai da dama na son zuwa jami'ar Teesside saboda suna da ta yi ta wajen karatu a duniya.
"Wajibi ne duk ɗaliban da ke fitowa daga ƙasar waje su samar da shaidar cewa suna da isassun kuɗin da za su biya kuɗin makaranta da na harkokin yau da kullum a matsayin wani sharaɗi na samun visa."
Jami'ar na taimaka wa ɗalibai dangane da damuwar da kowa ya samu kansa a ciki game da matsalar tattalin arziƙin Najeriya.