Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Waiwaye: Sukar ƙudirin haraji da gurfanar da masu zanga-zanga a kotu
Wannan maƙale ce da ke kawo muku muhimman labaran da suka fi jan hankali a Najeriya cikin makon da muke bankwana da shi.
Gwamnonin Arewa sun soki Tinubu kan ƙudirin gyaran haraji
Wata sabuwar dambarwa ta ɓarke game da ƙudurin harajin VAT da Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya aike majalisar dokokin ƙasar, yayin da ƙungiyar gwamnonin arewacin Najeriya ta fito fili ta yi fatali da ƙudurin, musamman kan yadda za a fasalta rabon harajin.
A wani taro da gwamnonin arewacin ƙasar suka yi a Kaduna a makon nan, sun ce sabon ƙudirin ya saɓa wa muradun jihohin arewacin ƙasar, inda suka yi kira ga ‘yan majalisar yankin su yi watsi da shi a zauren majalisar dokokin ƙasar.
“Abin da ya sa ba mu yarda ba, shi ne saboda ana karɓar harajin VAT ne a hedikwatar kamfanonin, maimakon inda sauran rassan kamfanonin ke gudanar da ayyukansu ko sayar da kayayyakinsu,'' in ji shugaban ƙungiyar gwamnaonin Arewa, Muhammad Inuwa Yahaya.
A farkon watan Oktoban wannan shekarar ne Bola Tinubu ya aike da wasu ƙudurori huɗu kan tsare-tsaren kuɗi ciki har da ƙudirin harajin VAT gaban majalisar dokokin ƙasar domin neman amincewarta.
Ita ma a nata ɓangare majalisar tattalin arzikin ƙasar, ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaban ƙasa, tare da gwamnoni jihohin ƙasar 36 a matsayin mambobi, ta buƙaci shugaban ƙasar ya jingine ƙudurin.
To sai dai cikin wata sanarwa da fadar shugaban ƙasar ta fitar ranar Juma'a ta, shugaban ƙasar ya ce ba zai jingine ƙudurin ba, sai dai ya alƙawarta yin gyare-gyare a cikin ƙudirin a majalisar dokokin ƙasar da lokacin jin ra'ayin jama'a.
Kotu ta ba da belin yaran da gwamnatin Najeriya ta gurfanar kan zanga-zanga
Babbar kotun tarayya a Abuja babban birnin Najeriya ta bayar da belin mutum 67 cikin 76 da gwamnatin ƙasar ta zarga da cin amanar ƙasa sakamakon zanga-zangar da suka gudanar a watan Agusta.
Kotun ƙarƙashin Mai Shari'a Obiora Egwuatu ta saka wa kowannensu sharaɗin naira miliyan 10, da kuma gabatar da mutumin da zai tsaya wa kowa, wanda ta ce dole ne ya kasance ma'aikacin gwamnati mai matakin albashi na 15.
Sai dai mutum 27 cikin waɗanda aka gurfanar a kotun ƙananan yara ne da shekarunsu ba su kai 18 ba, har da ma mai shekara 14, kamar yadda BBC ta gani a takardun kotun.
An tura manyan cikinsu zuwa gidan yari, an kuma aika da yaran wani gidan kula da kangararrun yara har zuwa ranar 25 ga watan Janairu, inda za a ci gaba da shari'ar.
An sako likitar da aka yi garkuwa da ita a Kaduna bayan wata 10
Likitar nan da aka yi garkuwa da ita a jihar Kaduna, Dr Ganiyat Popoola ta shaƙi iskar ƴanci bayan shafe kimanin wata 10 a hannun masu garkuwa.
An sace Poppola -wadda ke aiki a asibitin ido na ƙasa da ke Kaduna - ranar 27 ga Disamban shekarar 2023 tare da mijinta, Nurudeen Popoola wanda sojan sama ne da ɗan'uwanta Folaranmi Abdul-Mugniy, amma a watan Maris aka sako mijinta, amma masu garkuwar suka ci gaba da riƙe likitar da ɗan'uwan nata.
A watannin baya ne ƙungiyar likitoci masu neman ƙwarewa suka shiga yajin aiki saboda nuna rashin daɗin su kan gaza ƙwato likitar a hannun masu garkuwa.
Matatarmu za ta iya wadatar da ƴan Najeriya - Dangote
Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya ɗora alhakin ƙarancin man fetur da ake samu a Najeriya kan dillalan man da ya ce ba su saya daga gare shi.
Dangote ya bayyana haka ne bayan wata ganawa da kwamitin shugaban ƙasa kan sayar da ɗanyen man fetur a Naira ga kamfaninsa cikin da makon da ya gabatan.
Sannan a wani ƙarin bayani da ya yi, ya ce, "mun ƙiyasta cewa Najeriya na buƙatar lita miliyan 30 zuwa 32 a kullum. Wannan ba matsala ba ce saboda yanzu haka muna da lita miliyan 500 a tankinmu, wanda ke nufin ko ba mu tace wani man ba, muna da man da zai wadatar da Najeriya na sama da kwana 12," in ji Ɗangote.
Ya ƙara da cewa a shirye matatarsu take ta samar da lita miliyan 30 ga ƴan Najeriya a kowace rana.
NNPC ya ƙara farashin man fetur
A dai makon da muke bankwana da shi ɗi ne kuma kamfanin NNPCL ya sake ƙara farashin man fetur a Najeriya, inda farashin ya koma naira 1,025 a jihar Legas, sannan ya koma naira 1,050 a Abuja.
Wannan ƙarin na zuwa ne kimanin mako uku bayan gidajen man sun ƙara farashin man a Legas daga naira 855 zuwa 998, sannan aka ƙara farashin a sauran jihohin
Hakan ya sa an samu ƙarin kuɗin man fiye da wannan farashi a wasu gidajen man 'yan kasuwa a faɗin ƙasar.
Kotu ta ɗage shari'ar EFCC da Yahaya Bello zuwa Janairu
A makon da ya gabatan ne kuma wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta ɗage sauraron ƙarar zargin almundahanar da EFCC ke yi wa tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, zuwa 21 ga watan Janairun 2025.
A zaman kotun na ranar Laraba, lauyan EFCC, Kemi Pinheiro SAN, ya ce yana da shaidu biyu da zai gabatar, sannan ya buƙaci kotun ta ci gaba da karɓar shaidu ba tare da wanda ake zargi ba ya amsa ko ya musanta zargin da ake masa ba.
Pinheiro ya ƙada da cewa, "haƙƙin amsa laifi ko musantawa ba dole ba ne, dama ce da za a iya ƙwacewa," inda ya ce wanda suke ƙara ya yi watsi da damarsa.
A nasa lauyan wanda ake ƙara, Michael Adoyi ya ce bai amince da wannan ba, inda ya ce buƙatar lauyan masu ƙara ta ci karo da wani hukuncin kotun da ake dako.
Tinubu ya naɗa Janar Oluyede muƙaddashin babban hafsan sojin ƙasa
A cikin makon ne dai Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya naɗa Manjo Janar Olufemi Olatubosun Oluyede a matsayin muƙaddashin babban hafsan sojin ƙasa.
Mai magana da yawun fadar shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya ce Olufemi zai ci gaba da riƙe muƙamin har lokacin da Janar Taoreed Lagbaja zai koma ƙasar.
Tun a makon da ya gabata rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa Janar Lagbaja yana jinya a wani asibiti a ƙasar waje bayan ta musanta rahotonnin da ke cewa ya rasu.
Kafin naɗa shi a muƙamin, Oluyede ne kwamandan runduna ta 56 da ke Jaji a jihar Kaduna.
Kotu ta hana CBN bai wa jihar Rivers kasonta na gwamnatin tarayya
Mai shari'a Joyce Abdulmalik na babbar kotun tarayya da ke Abuja ya umarci babban bankin Najeriya CBN da ya dakata da bai wa jihar Rivers kasonta daga asusun gwamnatin tarayya na wata-wata.
Mai shari'a Abdulmalik ya ce kuɗaɗen kason da gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara yake karɓa daga gwamnatin tarayya tun daga watan Janairu zuwa yanzu ya saɓa doka, kuma dole a dakatar.
Alƙalin ya ce gabatar da kasafin kuɗin da gwamna Fubara ya yi a gaban ƴan majalisar jihar guda huɗu kacal ya saɓa da kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999.
Wannan ya sa alƙalin ya buƙaci babban bankin Najeriya da akanta-janar na ƙasar da bankin Zenith da bankin Access da su tabbatar Fubara bai ci gaba da amfani da kason jihar na wata-wata ba.
To sai da gwamnatin jihar ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin.