Ko Putin ya mulki Rasha yadda ya kamata a shekara 25 da ya yi kan mulki?

    • Marubuci, Steve Rosenberg
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Russia editor
    • Aiko rahoto daga, Moscow
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

Ba zan manta ranar jajiberin shekarar 1999.

Ina aiki a matsayin mai shirya shiri a ofishin BBC da ke birnin Moscow. Kawai sai labari ya karaɗe ko'ina: Shugaban ƙasar Rasha Boris Yeltsin ya yi murabus.

Matakin da ya ɗauka ya zo wa kowa da mamaki, ciki har da ƴan jaridar Birtaniya a Moscow. Lokacin da labarin ya fito babu wani wakili a ofis. Hakan na nufin ni zan rubuta tare da karanta labarin a cikin labaranmu na BBC.

"Boris Yeltsin ya sha faɗa cewa zai kammala wa'adin mulkinsa," kamar yadda na rubuta. "A yau ya faɗa wa ƴan Rasha cewa ya sauya matsayarsa."

A lokacin ne na fara aiki a matsayin wakili.

Kuma farawar Vladimir Putin a matsayin shugaban ƙasar Rasha.

Bayan murabus ɗin Yeltsin, kamar yadda kundin tsarin mulkin Rasha ya tanada, Firaminista Putin ne ya zama muƙaddashin shugaban ƙasa. Watanni uku bayan haka, ya lashe zaɓen shugaban ƙasa.

Bayan barin fadar Kremlin, saƙon Yeltsin ga Putin shi ne: "Ka kula da Rasha!"

Na riƙa tuna waɗannan kalamai da Yeltsin akai-akai, a daidai lokacin da yaƙin Rasha da Ukraine ke daf da shiga shekara ta uku.

Saboda mamayar da shugaba Putin ya yi a Ukraine ta yi mummunan tasiri.

A ɓangaren Ukraine, an lalata mata gine-gine da kuma mutuwar mutane a faɗin birane.

Kusan kashi 20 na yankunanta na a hannun Rasha, kuma an ɗaiɗaita mutane miliyan goma.

Amma Ga Rasha, ita ma:

Tun bayan matakin da Vladimir Putin ya ɗauka na kaddamar da abin da ya kira "farmakin soji na musamman", Rasha ta gamu da asara da dama a fagen daga.

  • Birane da kuma garuruwan Rasha sun sha fuskantar hare-haren jirage marasa matuki akai-akai
  • Sojojin Ukraine sun mamaye wani ɓangare na birnin Kursk na Rasha
  • Takunkumai na ƙasa da ƙasa na matsin lamba ga tattalin arzikin Rasha
  • Wani abin ƙari shi ne, al'ummar ƙasar Rasha na cikin wani hali

Na kasance ina bayar da rahoto kan Putin tun bayan da zama shugaban ƙasa.

A ranar 31 ga watan Disamban 1999, waye ma zai ɗauka cewa sabon shugaban Rasha zai shafe gomman shekaru yana kan mulki har kawo yanzu? Ko kuma Rasha za ta shiga yaƙi da Ukraine da kuma takun tsaka da ƙasashen yamma?

So tari ina shiga tunani cewa watakila da tarihi zai yi daban idan da a ce Yeltsin ya ɗauki wani na daban domin ya gaje shi.

Abu ɗaya da zan ce kan abin da na sani shi ne: cikin sama da shekara 25 na ga irin Putin daban-daban.

Kuma ba ni kaɗai bane.

"Putin da na haɗu da shi, ya yi abubuwa masu kyau har da kirkiro da majalisar Nato da Rasha, amma na yanzu ya sha bamban da na baya," kamar yadda wani tsohon jami'in Nato Lord Robertson ya faɗa min a 2023.

"Mutumin da ya tsaya kusa da ni a watan Mayun 2002, sannan ya ce Ukraine ƙasa ce mai ƴanci wadda za ta yanke hukunci kan batutuwa na tsaronta, a yanzu shi ne mutumin da ya ce Ukraine ba ƙasa ba ce mai kashin kanta.

"Ina ganin Putin yana da babban buri ga ƙasarsa. An amince da Tarayyar Soviet a matsayin mai iko na biyu a duniya. Rasha ba za ta yi iƙirari ta ɓangaren ba. Kuma tana ji da kanta."

Wannan shi ne ɗaya daga cikin sauyi da za mu ce mun gani a wajen Putin: Burin da yake da shi na "Mayar da Rasha babbar ƙasa ta kuma yi aiki yanda ya kamata" (da kuma kare martabarta kan abin da wasu ke ganin cewa rashin nasara da Moscow ta yi a yaƙin cacar-baki) domin kasar te ƙere wa makwaɓatanta - da kuma ƙasashen yamma.

Fadar Kremlin na da wani bayani na daban.

Daga jawabai da ya yi, kalamai da ya furta, ta kasance Putin mutum ne da yake shiga fushi idan aka yi masa ba daidia ba, da kuma nuna damuwa kan tsaron ƙasarsa wanda ƙasashen yamma ke nuna ko-in-kula.

Amma shin Putin ya yi imanin cewa ya cika buƙatar da Yeltsin ya nema a wajensa na "kula da Rasha?"

A baya-bayan nan, na samu damar yin bincike don gano hakan.

Sama da sa'a huɗu cikin jawabinsa na karshen shekara, Putin ya gayyaceni domin yin tambaya.

"Boris Yeltsin ya faɗa maka cewa ka kula da Rasha," na tunawa shugaban ƙasar. "To amma ya batun irin asarar da Rasha ta yi a abin da ka kira 'farmakin soji na musamman' kan Ukraine, sojojin Ukraine a yankin Kursk da takunkumai da kuma hauhawarar farashi. Kana ganin ka kula da ƙasarka?"

"Eh," Shugaba Putin ya mayar da martani. "Kuma ba wai na kula da ƙasar kaɗai ba. Mun kuma fito daga cikin wani kangi."

Ya kwatanta Rasha a karkashin Yeltsin a matsayin ƙasar da ke rasa karfin ikonta. Ya zargi yamma da "nuna cewa suna son Rasha" lokacin Yeltsin yayin da a gefe guda "suke amfani da Rasha don cimma manufofinsu". Sai dai, shi Putin, "yana yin komai", in ji shi, "domin tabbatar da cewa Rasha ta zama ƙasa mai iko da kanta".

Ayyana kansa a matsayin mai kare ƴanci da kuma ikon Rasha: Shin yana yi wa kansa wannan kallo ne saboda irin abubuwan da suka faru a baya domin ƙoƙarin wanke kansa kan yaƙin da yake yi a Ukraine? Ko kuma shin Putin ya ma yarda da abin da hakan zai yi tarihin Rasha?

Ba na tsammani gaskiya. Ba yanzu ba. Sai dai ina ganin wannan tambaya ce mai muhimmanci.

Amsa ga batun zai yi tasiri na yanda za a kawo karshen yaƙin - da kuma inda makomar Rasha za ta dosa.