Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abinda ya kamata ku sani kan wasan Barca da Young Boys
Barcelona za ta karɓi bakuncin Young Boys ranar Talata a wasa na biyu da kowacce za ta kara a Champions League a bana.
Ranar Alhamis 19 ga watan Satumba, Monaco ta ci Barcelona 2-1, ita kuwa Young Boys ta yi rashin nasara 3-0 a hannun Aston Villa a gida ranar Talata 17 ga watan Satumba.
Barcelona na kokarin ganin ta yi nasara a karawar, idan ba haka ba za a doke ta karo uku a jere a Champions League, idan aka haɗa da wanda PSG ta ci a bara.
Wannan shi ne karon farko da za su kara a tsakaninsu a Champions League, inda Young Boys ta mamaye gasar Switzerland a kaka shida baya, amma ba ta kokari a 2024/25.
Barcelona wadda ta ci wasan La Liga bakwai a jere da fara kakar nan, na fatan komawa kan ganiya, bayan da Osasuna ta doke ta 4-2 ranar Asabar.
Kamar yadda kowa ke lissafi, Barcelona za ta yi nasara a kan Young Boys, sai dai tamaula ba tabbas komai zai iya faruwa.
Wannan shi ne karon farko da Barcelona za ta fuskanci ƙungiya daga Switzerland tun bayan wasa da Basel a 2008.
Barcelona ta kara da Young Boys sau shida a sada zumunta tun daga 1913, yayin da na baya-bayan nan da suka fuskanci juna shi ne a 1958.
Young Boys mai fama da kalubale a kakar bana, ba ta ci wasa ba a waje tun bayan nasara 5-0 a kan Limerick a 1960.
Idan kuma Lamine Yamal ya ci ƙwallo zai zama matashi mai shekara 18 da ya zura na biyu a raga karo biyu a jere a Champions League.
A wasan da Monaco ta doke Barcelona aka bai wa Eric Garcia jan kati, kenan ba zai fuskanci Young Boys a gasar ta zakarun Turai ta ranar Talata ba.
Waɗanda ke jinya a Barcelona sun haɗa da Gavi da Ronald Araujo da Andreas Christensen da Marc Bernal da Dani Olmo da kuma Fermín López.