Zaɓen sarauniyar kyau da sukuwar doki a cikin hotunan Afirka

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Wasu daga cikin zaɓaɓɓun hotunan Afirka da na ƴan nahiyar a wasu sassan duniya cikin makon da ya gabata.

 Miss Nigeria Chidimma Adetshina da Miss Denmark Victoria Kjær Theilvig

Asalin hoton, Hector Vivas / Getty Images

Bayanan hoto, Wadda ta zo ta farko a gasar sarauniyar kyau ta duniya, Victoria Kjær Theilvig, 'yar ƙasar Denmark da wadda ta zo ta biyu a gasar, Chidimma Adetshina 'yar Najeriya na dakon sakamakon matsayinsu a gasar, jim kaɗan bayan kammala ta.A ranar Asabar ne aka gudanar da gasar a birnin Mexico City na ƙasar Mexico.
 Ms Adetshina

Asalin hoton, Hector Vivas / Getty Images

Bayanan hoto, Duk da cewa Ms Adetshina ba ta lashe babbar kyautar ba, amma ta zo ta biyu. Ita ce mace baƙar fata ta da ta fi kowacce ƙoƙari a gasar tun bayan da ƴar Afirka ta Kudu Zozi Tunzi ta lashe gasar a shekarar 2019.
Marayun Giwaye

Asalin hoton, Gerald Anderson / Getty Images

Bayanan hoto, Giwaye da suka rasa Iyayensu ta hanyar farauta, suna wanka a cikin laka a gandun dajin Nairobi na ƙasar Kenya.
Makaɗan  gargajiya a ƙasar Burundi

Asalin hoton, Badru Katumba / AFP

Bayanan hoto, Makaɗan gargajiya a Burundi sun yi wasa a rana ta uku na bikin Nyege Nyege na shekara-shekara wanda ke murnar bayyanar sabbin masu nuna bajinta a garin Jinja na Uganda.
Masu raye-raye a Burundi

Asalin hoton, Badru Katumba / AFP

Bayanan hoto, Ɗaruruwan masu raye-raye sun baje kolin basirarsu a wurin bikin.
Wasannin nishaɗi  a Burundi

Asalin hoton, Badru Katumba / AFP

Bayanan hoto, Baya ga kaɗe-kaɗe da raye-raye an gudanar da wasannin nishaɗi da dama a wurin bikin
Wata mata ƴar ƙasar Mozambique ta zana tutar ƙasar a fuskar ɗanta

Asalin hoton, Horacio Villalobos / Getty Images

Bayanan hoto, Wata mata ƴar ƙasar Mozambique ta zana tutar ƙasar a fuskar ɗanta yayin da suke fitowa kan titunan Lisbon babban birnin ƙasar Portugal domin nuna adawa da zaɓen da ake taƙaddama kan sakamakonsa.
Habiba Aly ta Masar ta fafata a gasar wasannin motsa jiki ta ƙasa da ƙasa a Doha, Qatar.

Asalin hoton, Noushad Thekkayil / Getty Images

Bayanan hoto, A ranar Laraba, Habiba Aly ta Masar ta fafata a gasar wasannin motsa jiki ta ƙasa da ƙasa a Doha, Qatar.
Matuƙin ''boda boda'' (ɗan Acaɓa) a Birnin Kampala, Uganda

Asalin hoton, Michele Spatari / AFP

Bayanan hoto, Matuƙin ''boda boda'' (Acaɓa) ya kishingiɗa kan babur ɗinsa a Birnin Kampala, Uganda ranar Juma'a
Masu sukuwa a birnin Oued Souf na Aljeriya.

Asalin hoton, Abdelaziz Boumzar / Reuters

Bayanan hoto, Masu sukuwa suna jira don fara wasan sukuwar doki a bikin yawon buɗe ido na ƙasa da ƙasa a birnin Oued Souf na Aljeriya, ranar Asabar